✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara bajekolin shinkafa a Kanonai da ayyukan Gona ta Jihar Kano tare da haxin gwiwar Qungiyar Games4 suka qaddamar da bikin bajekolin shinkafa a Jihar Kano. Bajekolin wanda shi ne irinsa na farko ya samu halartar kamfaninninkan casar shinkafar gida da

A shekaranjiya Laraba ne Cibiyar Ciniki, Ma’adinai da ayyukan Gona ta Jihar Kano tare da hadin gwiwar kungiyar Games4 suka kaddamar da bikin bajekolin shinkafa…

A shekaranjiya Laraba ne Cibiyar Ciniki, Ma’adinai da ayyukan Gona ta Jihar Kano tare da hadin gwiwar kungiyar Games4 suka kaddamar da bikin bajekolin shinkafa a Jihar Kano.

Bajekolin wanda shi ne irinsa na farko ya samu halartar kamfaninninkan casar shinkafar gida da suka hada da Miba rice Uza Rice da sauransu wadanda suka baje hajarsu ga masu saye. A jawabinsa wajen bude taron Shugaban Cibiyar Ciniki da Ma’adinai da Ayyukan Gona ta Jihar Kano, Alhaji Rabiu Umar dan Suleka ya bayyaana cewa sun shirya bajekolin ne da niyyar sama wa kamfaninnikan kasuwa ta yadda za su hada su da ‘yan kasuwa domin kasuwancin shinkafa ya bunkasa a jihar.
Shugaban ya yi fatan cewa nan da ’yan shekaru kalilan, Najeriya za ta kasance kasar da za ta rika fitar da shinkafa kasashen waje a maimakon shigo mata da shinkafa da ake yi.
Shi ma a nasa jawabin Shugaban Kwamitin gudanar da wanann bajekoli na kungiyar Games4 Tunde Ojerede ya bayyana cewa makasudin shirya wannan bajekoli shi ne don a “bunkasa tare da ciyar da shinkafar gida gaba,” inji shi. Da yake bayyana dalilin da ya sa kungiyarsu ta zabi Jihar Kano a matsayin magwajin wanann bajekoli saboda kasancewar jihar babba kasuwar shinkafa. “Idan aka yi la’akari da kasancewar Jihar Kano ta tara a yawan manoman shinkafa da kamfaninnikan casar shinkafar da kuma kasuwancinta hakan ya sa muka zabi jihar a matsayin wurin farko da za mu fara gudanar da wanann bajekoli don samun karbuwarsa a saurana jihohin kasar nana baki daya,”inji shi.
Daga nan ya yi kira ga manoman shinkafa da su kara himma tare da sanya jari a cikin harkar, kasancewar a yanzu ana kokarin ganin an sama musu kasuwa ta yadda wanann shinkafa za ta samu karbuwa: “Idan na ga manoma na jin tsoron yin noman shinkafar da yawa, to muna yi musu albishir da su saki jiki su yi noma sosai, domin muna fatan za su dara a nan gaba kayansu za su shiga ba tare da yin asara ba,” inji shi.
Shi ma a nasa jawabin daya daga cikin kamfaninnikan da ke aikin casar shinkaf, wakilin kamfanin Miba Rice Alhaji Mahmud Hassan ya bayyana cewa sakamakon samar da injinan aikin cassar shinkafa masu inganci da suka yi a yanzu shinkafar gida ta inganta yadda za a ta iya yin kafada-kafada da duk wata shinkafa da wasu kasashen wajen ke yi. “A yanzu ba kamar a lokacin baya ba shinkafar gida za ka same ta babu buntu, babu bukus ballantana tsakuwa. Yanzu shinkafarmu ta zama daga buhu sai tukunya. Haka kuma mun inganta ta ta hanyar sanya ta a buhuna masu inganci da suka kama daga kilo daya ko kilo biyu kai har zuwa kilo hamsin,” inji shi.