Mahaman Lawan Gaya shi ne Sakatare Janar na Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur na Nahiyar Afirka (APPO) kuma yana daya daga cikin wadanda suka samu nasarar cin jarrabawar neman jagorancin kungiyar. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana nasarorin da kungiyar ta samu a cikin shekara uku da zabansu.
Ko za ka gabatar da kanka a takaice?
Sunana Mahaman Laouan Gaya, Sakatare Janar na Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur na Nahiyar Afirka wato African Petroleum Producers’ Organization (APPO) wadda ke da hedkwata a da a Brazzabille da ke Kongo, amma yanzu take da ofishinta a Abuja.
Yaushe aka kafa wannan kungiyar?
An assasa kungiyar APPO a ranar 27 ga Janairun shekarar 1987 a Jihar Legas. Ta fara da mambobi 18 daga kasashen Afirka masu arzikin man fetur. Kungiyar APPO kungiya ce mai zaman kanta. Na fara jagorancin kungiyar a watan Yulin shekarar 2015. Kasancewar tun kafa kungiyar sama da shekara 25 ba ta yi wani tasiri ba ya sa aka sake canja wadanda za su jagoranci kungiyar. Daga bisani kungiyar ta yanke shawarar ta bude ofishinta a Abuja don samun cikakken goyon baya daga sauran kasashen Afirka.
Mane ne ayyukan kungiyar?
Tsarin kungiyar APPO sun hada da neman hadin gwiwar kasashen Afirka kan yadda za a bullo da hanyoyin bunkasa tattalin arzikin man fetur a kasashen da ke da arzikin man fetur. Mambobin kungiyar sun kai kashi 12 cikin 100 na kasashe masu arzikin man fetur a duniya. Daya daga cikin manufofin kungiyar APPO shi ne bunkasa tattalin arzikin kasa, hakan zai sa kasashen Afirka su kara samun kudin shiga.
Babban burin kungiyar APPO shi ne ta tabbatar an fi samun ribar kudin man fetur fiye da komai a Afirka. Kuma kungiyar na kokarin dakile kalubalen tsaro, da karancin abinci da dai sauran matsalolin da kasashen Afirka ke fuskanta. Idan har shugabanin kasashen Afirka za su bayar da goyon baya, za mu iya wuce sauran kasashen Larabawa a harkar kasuwancin man fetur. Matsalolin da kungiyar fuskanta tun lokacin da aka kaddamar da ita sun hada da rashin goyon baya a gwamnatance. Sama da shekara 25 kungiyar ba ta samun cikakkenn goyon baya daga shugabanni ba. Yanzu lokaci ne da Afirka za ta san muhimmancin man fetur da bunkasar tattalin arziki.
Wane irin nasarori kungiyar ta samu tun lokacin da aka zabe ku?
Tun lokacin da aka kirkiro kungiyar ba ta yi wani tasiri ba. Da yake ba a mayar da hankali a kanta ba tun lokacin aka kaddamar da ita ba, sai aka duba wane irin matakai za a dauka don sake tsarata. Da za a dauki sabon Sakatare Janar sai da aka yi jarrabawa, bayan an kammala aka daukeni a ka bani jagoroncin wannan kungiyar. Bayan shekara uku muna aiki, aka ga mun kawo sauyi sai ministoci suka taru a kasar Angola a shekarar 2015 suka ce lallai idan ana so wannan kungiya ta karfafa, suna so a sake habbakata domin bunkasa tattalin arzikin kasashenmu, sai aka ce dole sai an samu babbar kasa wadda za ta ba mu goyon baya, daga nan ministoci suka ce kasar da za ta iya ba mu goyon baya ita ce Najeriya, shi ya sa muka taso daga kasar Kongo muka dawo Najeriya, ta yadda za a karfafa wannan kungiyar.
Abin da nake fata shi ne kafin mu kammala wa’adinmu mu gudanar da taron da za a gayyaci shugabannin kasashen Afirka da wadanda suke kula da harkokin man fetur a kasashen. Idan aka yi hakan za mu gabatar da bukatun kungiyar da abin da take da shi. Hakan zai iya sa mu samu goyon baya daga sauran kasashen. Abin da ya sa kungiyar ba ta yi gagarumin taron ba shi ne shugabannin kasashe ba su ba kungiyar goyon baya, amma tunda yanzu an fito da sabbin tsari da shugabanni za su bayar da goyon baya, in Allah Ya yarda badi za mu taka muhimmiyar rawa.
Wane irin sauyi kungiyar ta samu?
A cikin sauyin da aka samu a akwai gano abubuwan da suke hana ruwa gudu, kuma mun fara magance su. Shi ya sa tun da farko da muka karbi shugabancin muka ga tsarin da kungiyar take, muka duba yadda ma’aikatan kungiyar da yadda ake kashe kudi da karin kudin ma’aikata na kungiyar. Sai muka tabbatar da tarurrukan da ake yi an dauke su da muhimmanci kuma an amince wa wadanda za su iya daukan matakai saboda mu gyara al’amura.
A wasu wuraren har yanzu ba a san kungiyar ba, amma idan ka ce OPEC wato Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur ta duniya kowa ya santa. Wannan yana kawo cikas saboda ba a dauketa da wani muhimmanci ba. Don haka muka fara ganawa da ‘yan jarida don bayyana manufofin kungiyar. Wannan kungiya ba tamu kadai ba ce, ta duk ‘yan kasashen Afirka ce. Mu samu mu habbakata, don haka take neman goyon baya daga shugabannin kasashen Afirka.
Mene ne bambancin Kungiyar APPO da OPEC?
Muna aiki tare da OPEC, amma ayyukanmu sun bambanta. Kasashen OPEC akwai wadanda suka fito daga Nahiyar Afirka akwai yankin Amurka sannan akwai kasashen Asiya sannan akwai na Larabawa. Ayyukan OPEC shi ne su lura da farashin danyan man fetur. Ya kamata mu hada gwiwa tsakanin ayyukan Kungiyar APPO da OPEC. Saboda idan suka rage yawan man da suke hakowa duk farashin man duniya sai ya tashi. Idan suna so a rage farashin man fetur man da suke hakowa sai su kara ko da kadan ne. Amma kungiyar APPO ayyukanta na kasashen Afirka ne kawai, APPO tana da hadin gwiwa ne da sauran kasashen Afirka don taimakawa sauran kasashen da ba su da man fetur, akwai hadin gwiwa a tsakaninmu don bunkasa tattalin arzikin kasashenmu. Yayin da su kuma OPEC hakkin su ne lura da farashin man fetur, ita APPO an kirkire ta ne don hadin gwiwa a tsakanin kasashen Nahiyar Afirka.
A karshen wa’adin shugabancinku me kuke fatan cin ma nasara?
Idan har za mu samu goyon bayan da muke bukata, za mu iya wuce Saudiya da kasashen yankin Amurka a harkokin kasuwancin man fetur. Ba kawai za mu dubi farashin man fetur kadai ba ne, har da harkar tsaro a Afirka. Dole mu yi la’akari da yanayin farashin mai a kasuwanninmu. A yanzu haka wasu kasashen sun fara fitar da maI, amma zuwa wani lokaci zai iya karewa. Amma a Afirka muna da danyan mai mai yawa. Burinmu shi ne mu tabbatar da ana iya fitar da kashi 30 cikin 100 na tattalin arziki daga Nahiyar Afirka, akwai ayyuka da dama a fannin man fetur.