Babbar Kotun Tarayya ta Katsina ta daure wasu ‘yan Najeriya watanni uku-uku a saboda laifin shiga Jamhuriyar Nijar ba bisa ka’ida ba.
Hukumar shige da fice ta Najeriya ta gurfanar da mutanen su 12 ne bayan sun tsallake iyakar Jamhuriyar Nijar ta barauniyar hanya amma aka kama su aka dawo da su Najeriya.
Da take yanke hukumci bayan masu laifin su amsa laifukansu, Mai Shari’a Hadiza Shagari ta ba kowanensu zabin biyan tarar Naira dubu hamsin ko zaman kurkuku na wata uku.
Lauyoyin masu laifin da masu gabatar da kara, Barista Najib Abdullahi da Barista Obilor Collins duk sun aminta da hukuncin kotun.
Aminiya ta ruwaito cewar wadanda aka yanke wa hukumci ‘yan asalin jihohin Inugu da Edo da Legas da Ribas da Ogun da Delta da kuma Abiya ne.
Suna kuma daga ciki mutum 42 da aka maido Najeriya ta iyakar Jamhuriyar Nijar da ke Kongolam.
Za kuma a gurfanar da sauran mutum 30 a gaban kuliya idan aka gama tantance su.