Wani dan kasuwa mai shekaru 40 ya shiga hannun hukuma bayan an kama shi dumu-dumu yana lalata da ’yarsa mai shekara biyar da yayarta mai shekaru bakwai.
Wata kotun majistare da ke Ikeja babban birnin jihar Legas, a ranar Laraba, ta bayar da umarnin tsare magidancin a gidan yarin a Kirikiri bisa zargin lalata da ’ya’yansa mata biyu.
Mai Shari’a, Misis Bola Osunsanmi, ta ki sauraron wanda ake kara, ta dage shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Yuni.
Ta ce za ta saurari shawara daga Daraktan shigar da kara na kasa kafin wannan lokacin.
Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya NAN ya bayyana cewa tun da farko, dan sanda mai gabatar da kara, ASP Raji Akeem, ya shaida wa kotun cewa a watan Satumba na 2021, matar wanda ake kara ta kama shi yana lalata da ’yarsu mai shekara bakwai.
Yayin da a watan Mayu, 2024, matar ta kara kama shi yana kokarin lalata da wata ’yar tasu mai shekaru biyar.
Abin da ya fusata ta, ta kai karar sa ga hukuma.
Mai gabatar da karar ya ce, wadannan laifuka sun saba wa sashe na 137 na dokar laifuka ta jihar Legas da aka inganta a 2015.