✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daure matashi bisa yi wa Sarkin Kano sojan gona

Kotun Majistare ta 29 da ke Nomaslan a birnin Kano ta daure wani matashi shekara daya a kurkuku saboda samunsa da yi wa Mai martaba…

Kotun Majistare ta 29 da ke Nomaslan a birnin Kano ta daure wani matashi shekara daya a kurkuku saboda samunsa da yi wa Mai martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II sojan gona ta hanyar yin amfani da shafin zumunta na facebook.

Tun farko ’yan sanda ne suka gurfanar da matashin mai suna Sultan Bello a gaban kotun, inda aka tuhume shi da bude shafin sada zumunta na facebook a matsayin Mai martaba Sarkin Kano, inda yake maganganun da ba su kamata ba a shafin.

Bayan karanto masa laifuffukansa, wanda ake zargin ya amsa dukan laifuffukan uku da ake zarginsa da su da suka hada da laifin cuta da na sojan gona da kuma na bata suna. Laifuffukan da suka saba wa sashe na 322 da na 187 da  na 291 na  Kundin Shari’a na Final Kod. Alkalin Kotun, Mai shari’a Hassan Ahmad ya yanke masa hukuncin daurin ko kuma ya biya tarar Naira dubu 30.