Kotu ta yanke wa wata budurwa da saurayinta hukuncin dauri da aikin karfi na wata biyu bisa laifin garkuwa da kansu da suka yi.
Kotun Majistire da ke zama Ado Ikiti, ta yanke wa Mary Idris da masoyinta Victor Olawusi masu shekara 20-20 hukuncin tare da umartar a basu shawarwari na tsawon mako biyu akan laifin da suka aikata.
Mai gabatar da kara, Monica Ikebulo, ta ce masu laifin “Sun nemi tayar da hankalin mutane ta hanyar boye kansu da karyar an yi garkuwa da ita don karbar kudin fansa daga hannun iyayen Mary”.
Ta ce Mary ta wajen saurayinta don su sheke ayarsu ne a Akure, amma da kudin suka kare ta rasa yadda za ta yi ta dawo gida Ado Ikiti, sai suka tura suka tura wa mahaifanta rubutaccen sakon cewa an yi garkuwa da ita, kuma sai sun biya kudin fansa.
Mary ta je Ado Ikiti daga Akure ta Jihar Ondo, ranar 9 ga watan Agusta, 2020 inda suka hada kai da Victor suka tura wa mahaifanta sakon.
Mai Shari’a, Adefunke Anoma, ya ce “hakan abun bakin ciki ne, kuma yana nuna da yadda al’umma ta lalace”.
Ya yi tir da matakin da budurwar ta dauka na barin gidansu zuwa gidan hutu da ta kwashe kwana hudu.
“Budurwa da saurayin za su yi aikin karfi da karbar shawarwari. Za su yi zaman wakafin a jere su kuma dawo a lokacin da aikin nasu ya kare,” inji mai shari’ar.
Ya kuma ce, Shugaban tsaro na Ma’aikatar Shari’ar Jihar Ikiti zai kula da aikin karfin, sai rijistaran Kotun ya kula da shawarwarin.