Wata kotu ta samu Abdallah kassem, dan kwallon Hadaddiyar Daular Larabawa da laifin zagin kocinsa al’amarin da ya sa aka daure shi wata kotu ba tare da zabin tara ba.
Kamar yadda wata jaridar da ake wallafawa a Dubai ta kalato, an ga dan kwallon a wani hoton bidiyo ne yana gyadawa kocin kai da kuma yi masa gyatsine da hakan ya nuna yana zaginssa saboda bai sanya sunansa a ’yan kwallon da suka buga wani wasa ba.
dan kwallon mai kimanin shekara 29 yana buga wa kulob dinAl-Dhafra na Dubai kwallo an ce ya zagi kocinsu ne bayan kocin ya ki gayyatarsa a cikin wadanda za su yi wa kulob din kwallo.
kassem tare da wani takwaransa da ake zargin shi ya dauki hoton bidiyo a lokacin da dan kwallon ke zagin kocin sannan ya watsa a kafar sadarwar intanet da hakan ta janyo hankalin mahukunta kulob din da kocin inda kocin ya shigar da kara kuma kotu ta same su da laifi kuma aka yanke musu hukuncin daurin watanni uku kowannensu.
Kotun ta ce ta same su da laifin yin amfani da na’urar sadarwa irin ta zamani ne wajen yin abin da zai iya tayar da hankalin al’umma al’amarin da ya sa aka yanke musu wannan hukunci.
Rahoton da wata jarida da ake wallafa wa a Dubai ta kalato ya nuna tuni kulob din ya dakatar da ’yan kwallon biyu sai dai Lauyan kassem ya ce ba da sani ko izinin dan kwallon ne aka saki faifan bidiyon har jama’a suka gani ba. Sannan Lauyan ya ce hatta shi kansa koci Ali ba shi da niyyar ruruta maganar don haka akwai yiwuwar ya janye karar.