✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An damfari mutum 500 da takardun aiki na bogi a Cibiyar Cutar Tari Fuka ta Zariya

Kimanin mutum 500 ne aka samar wa takardun aiki na bogi a Cibiyar Kula da Tarin Fuka da Cutar Kuturta ta Kasa (National Tuberculosis and…

Kimanin mutum 500 ne aka samar wa takardun aiki na bogi a Cibiyar Kula da Tarin Fuka da Cutar Kuturta ta Kasa (National Tuberculosis and Leprosy Training Center) da ke Saye a Karamar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna.

Cikin wadanda ake zargi da damfarar har da matar Shugaban Cibiyar mai suna Madina da Nazifi Adamu wanda ake zargi da samar da takardun da ke dauke da tambarin cibiyar na jabu (Letter headed), sai Yusuf Alhaji da ake zargi da sanya hannun irin na Daraktan Cibiyar, sai Musa Sokodibo da ake zargi da samar da lambar albashi (IPPS) sai Adamu Maiwada Aliyu da Suleiman Adamu da  Abubakar Ibrahim.

Aminiya ta samu labarin cewa an bankado lamarin ne lokacin da aka zo daukar bayanan sababbin ma’aikatan da aka dauka daga Abuja don shigar da su cikin wadanda za a biya albashi na Gwamnatin Tarayya, shi ne wadannan mutane suka taho da takardunsu amma sai aka ce babu sunansu a cikin ma’aikatan.

Jin haka sai suka bayyana cewa wadansu daga cikin ma’aikatan cibiyar ce suka sayar musu da takardun daukar aiki a kan Naira dubu 200 zuwa Naira dubu 500, gwargwadon matsayin da aka dauki mutum.

Aminiya ta ji ta bakin wadansu daga cikin wadanda aka damfara da aka dauke su aiki, ko ’ya’yansu inda suka bayyana wa wakilinmu cewa suna jiran sakamakon binciken ’yan sanda ne don haka ba za su ce komai  ba a yanzu.

Aminiya ta gano cewa daga cikin wadanda aka karbi kudadensu har akwai wanda ya ba da kudi Naira dubu 700 na ’ya’yansa biyu, kuma akwai wanda ya ba da Naira dubu 500, wadansu kuma shanun da suke kiwo suka bayar aka ba su ‘aikin’. Majiyar Aminiya ta ce sama da mutum 902 ne aka ba takardun daukar aikin na bogi, amma mutum 400 kawai za a dauka, sannan majiyar ta ce wadansu kuma an ba su takardun daukar aikin amma suka sayar.

Majiyar Aminiya ta ce kudin da ake zargin an karba a hannun mutane ya kai Naira miliyan 25.

Da Aminiya ta tuntubi Daraktan Cibiyar, Dokta Labaran Shehu ya ce wadanda suka aikata zambar sun yi ne don son zuciyarsu, kuma suna hannun ’yan sanda domin bincike kuma bada yawun wani jami’in cibiyar suka yi ba.

Da yake tabbatar da kama  ma’aikatan, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Yakubu Aliyu Sabo ya tabbatar da haka, inda ya ce ofishin yankinsu da ke Saye sun turo mutanen zuwa Kaduna, kuma ana ci gaba da bincike.