✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dakatar da Mourinho saboda daga wa alkalin wasa murya

Mourinho ya yi wa alkalin wasa Luca Pairetto ihu.

An dakatar da Jose Mourinho daga halartar wasanni biyu, bayan da alkalin wasa ya bashi jan kati saboda bacin ran da kocin ya nuna yayin wasan da AS Roma ta yi da Verona a gasar Seria A.

A ranar Talata ce Mourinho ya yi wa alkalin wasa Luca Pairetto ihu, tare da kwaikwayon kiran wayar da aka yi masa, abin da ya kai ga ba shi jan kati.

Kafofin yada labaran Italiya sun ruwaito cewa Mourinho bai ji dadin yadda aka kara lokaci kadan ba a ranar Asabar, yayin wasan da aka tashi 2-2 tsakanin kungiyarsa ta AS Roma da Verona.

A yanzu Roma ta koma tazarar maki shida tsakaninta da Juventus wadda ke matsayi na hudu a gasar zakarun Turai.