✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An dakatar da Makaman Katsina

Dakatarwar ta fara aiki ne daga ranar Laraba 23 ga watan Nuwamba da muke ciki.

Masarautar Katsina ta dakatar da Makaman Katsina Hakimin Bakori. Alhaji Idris Sule Idris, daga kujerarsa har sai an gama bincike a kansa.

Masarautar ta ce dakatarwar ta fara aiki ne daga ranar Laraba 23 ga watan Nuwamba da muke ciki.

Sanarwar dakatarwar da aka raba wa ’yan jarida dauke da sa hannun Mataimakin Sakataren Masarautar, Alhaji Sule Mamman Dee (Sarkin tsabta), ba ta yi bayani a kan abin da za a binciki basaraken ba.