✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dakatar da dan sandan da ya harbe lauya a Legas daga aiki

Dakatarwar da aka yi wa jami'in ta soma aiki ne take ba da bata lokaci ba.

Hukumar Kula da Harkokin ‘Yan Sanda (PSC), ta dakatar da dan sandan da ake zargi da kashe lauya Bolanle Raheem da bindiga a Legas.

Dakatarwar na kunshe ne cikin  sanarwar da hukumar ta fitar ta bakin shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a, Mista Ikechukwu Ani, ranar Alhamis a Abuja.

Sanarwar ta ce dakatarwar da aka yi wa jami’in ta fara aiki ne take ba da bata lokaci ba.

Haka nan, hukumar ta ba da umarnin a yi binciken karshe kan badakalar domin daukar mataki na gaba.

Ani ya ce, bayan nazari cikin nutsuwa da hukumar ta yi wa lamarin ta aike wa Sufeto-Janar na ’Yan Sanda da wasika inda ta samu amincewarsa kan a dakatar da jami’in da lamarin ya shafa ba tare da bata lokaci ba.

Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito yadda dan sanda ya dirka wa marigayiyar bindiga ranar Kirsimeti a Legas, lamarin da ya ja hankalin jama’a a gida da wajen kasa.