✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dage auren matashi dan Kano da masoyiyarsa baturiyar Amurka

An dage daurin auren matashin nan dan jihar Kano Isa Sulaiman da masoyiyarsa baturiyar Amurka Jeanine Sanchez wanda a baya aka shirya yi a watan…

An dage daurin auren matashin nan dan jihar Kano Isa Sulaiman da masoyiyarsa baturiyar Amurka Jeanine Sanchez wanda a baya aka shirya yi a watan da muke ciki bayan da ta ziyarce shi a gidansu da ke Fanshekara a watan Janairun da ya gabata.

Mahaifin matashin Malam Sulaiman Isa ne ya shaidawa Aminiya hakan, ta wayar salula inda ya ce an dage daurin aure, ba a kuma sake sanya rana ba sai zuwa lokacin da baturiyar zata samar masa takardun izinin zama ƙasar Amurka, ya ce dage daurin auren ya biyo bayan matakin hana wa ‘yan Najeriya biza da kasar Amurka ta dauka.

Sulaiman, mai shekaru 25 wanda ke karatu a jami’ar Bayero ta Kano ya shirya auren masoyiyarsa baturiyar Amurka mai ‘ya’ya biyu bayan sun hadu da ita a kafar sada zumunta ta instagram kimanin shekara guda da ta shude inda ya yi niyyar ci gaba da karatunsa a Amurka bayan an daura auren nasu.