✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ciza a hura

Ita dai gaskiya dadi ke gare ta, kuma duk yadda aka yi kokarin a kauce mata sai an komo kanta. Wannan bayani ya yi daidai…

Ita dai gaskiya dadi ke gare ta, kuma duk yadda aka yi kokarin a kauce mata sai an komo kanta. Wannan bayani ya yi daidai da yadda kissar Babachir Dabid Lawal da Ayo Oke  ta kaya, mutanen da aka zarga da  aikata masha’a a bakin aikinsu, aka kuma kafa hukumar bincike mai karfin gaske  domin ta binciko gaskiyar al’amarin. An gano gaskiyar, an kuma bi hanyar gaskiya wajen yin abin da ya fi dacewa, an kuma fahimci cewa gaskiyar ta yi halinta ta fuskoki da yawa. 

Da farko dai ana iya cewa sakamakon da ya biyo bayan rahoton binciken da kwamitin Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yomi Osinbajo ya yi ya kara tabbatar da cewa yakin da ake yi da rashawa da gaske ne ba da wasa ba, duk kuwa da cewa ana ta korafin yin bori da sanyin jiki dangane da haka. Ga shi nan a karon farko an kwakkwabe wasu kusoshin gwamnatin tarayya daga aikinsu saboda an bincika, an same su da aikata laifin da ake yaki da shi, an kuma ba hukumomin ladabtarwa damar yin wasan kura da su domin su dandana kudarsu, a kuma ingiza keyarsu gidan jarun idan ta kama a yi haka. Talakawa na jiran su ga yadda za ta sake kayawa a wancan bangaren, domin kuwa idan an kashe maciji to wajibi ne a sare kan don kada wasu su taka, su kwashi dafi. 

A game da dogon jinkirin da ake ta kwakwazo akai kafin a dauki matakin aiwatar da rahoton kwamitin Farfesa Osinbajo,  ana iya cewa an dai yi, kuma biyan bukata ya fi dogon buri. An kwatanta gaskiyar da ta kwantar da zukatan jama’a da yawa game da haka. 

Ashe ke nan ana iya cewa wani babban darasi ya fito daga matakin da gwamnati ta dauka game da wancan rahoton, musamman ma a daidai lokacin da ‘yan adawa ke cewa su ne aka fi bincika, ake kuma kuntatawa, ana barin ‘ya’yan jam’iyyar da ke da gwamnati, wadanda su ma ba su tsira ba daga irin zarge-zargen da ake yi musu na almundahana da dukiyar al’umma, amma sai ga shi nan gwamnati na da manufofi guda biyu mabambanta game da wadanda take zarga da kuma zargowa don bincike. daya wacce ake aiki da ita domin ‘yan adawa daya kuma wacce aka kebe don ‘yan jam’iyya mai gwamnti.

Ana iya cewa a wannan karon dai dara ta ci gida, domin kuwa ga shi nan wani jigo na  ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki  ne da kuma wani hamshakin ma’aikacin gwamnatin tarayya aka tasa a gaba, aka kuma ga bayansu saboda an tabbatar da laifin da aka zarge su da aikatawa. Abin sha’awa game da haka shi ne Majalisar Dattijai, wacce a cikinta ‘ya’yan jam’iyyar APC wacce ke da rinjaye, ta fara daukar matakan binciken zarge-zargen da aka yi wa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya game da mundahanar da ya yi da dukiyar da aka danka masa amana, bisa ikon da take da shi na bincika al’amura irin haka. 

Rahoton binciken wani kwamiti na musamman ne da majalisar dattijan ta kafa  a karkashin shugabancin Sanata Shehu Sani ya tabbatar da zarge-zargen da aka yi wa Babachir Dabid Lawal, kuma hakan ne ya sa Shugaban kasa kafa kwamitin bincike. Idan aka yi la’akari da kyau za a fahimci cewa Babachir Lawal da aka zarga da cin kudin yanke ciyawa  da Sanata Shehu Sani  da ya zame cinnakan da bai san na gida  da  kuma Shugaba Muhamadu Buhari, kaifi daya wanda ya raja’a ga bangaren gaskiya, dukkansu ‘ya’yan jam’iyyar APC ne,  wadanda ake zargin cewa su shafaffu da mai ne wadanda ake zargin cewa  ba a bi ta kansu da batun bincike. 

Hakika, an yi nisa da  yaki da rashwar da aka faro  fiye da shekaru biyu a kasar nan, an kuma zazzargo mutane da yawa da aka bincika aka samu da laifuffukan da suka kamata a ce suna  yi wa alkalan kotuna ne bayanai game abubuwan da suka sani; wadansu kuma da tuni sun san makomarsu, har sun tsufa a gidan kaso, bayan yanke musu hukunci. Talakawa na sane da cewa akwai wasu da aka dandanko game da dukiyar talakwan da suka zakalkala, amma sun mayar da wasu daga ciki ga hukuma salun-alun, bakinsu kanin kafarsu, don su tsira da dan mutuncin da ya rage musu, amma akwai wasu da har yanzu ake ja-ni-in-ja-ka game da dukiyar da suka yi rub-da-ciki bisanta, sun ki su daga, sa’annan  shari’a kuma ba ta hau kansu ba, domin  ana ta janjani game da gurfanar da su a gaban shari’a.

Akwai kuma batun wasu da suka dade a hannu, ana kuma ci gaba da bincikensu  bayan an dankwafar da su gaban shari’a, amma har yanzu maganarsu ba ta kaya ba balle su san makomarsu. Game da irin wadancan mutanen ana iya cewa jinkirta hukunci tamkar muzanta shari’a ne, domin bayar da dama ga mutumin da ake zarga ya san makomarsa ni’ima ce a gare shi, domin hankalinsa zai kwanta, ‘yanuwa da dangoginsa kuma za su yi amanna da  kaddarar da ta afka masa, walau mai kyau ko mara kyau ce. 

Dangane da haka nan ana iya yin kira ga jami’an tsaro da ke binciken shari’o’in wasu fitattun ‘ya’yan jam’iyyar adawa da su gaggauta kawo karshensu, kamar wadanda suka shafi  tsohon mai bayar da shawara ga tsohon shugaban kasa game da harkokin tsaro, Kanar Sambo Dasuki, mai ritaya da kuma tsohon Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar PDP, Cif  Olisa Metuh, domin haka ne zai ba kotuna damar sauraron kararrakin da ke gabansu game da su sa’annan kuma su gagauta yanke hukunci. Dukkan wadannan mutanen guda biyu sun ambato sunan tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a matsayin wanda ya ba da umurnin firfitar da kudaden da ake zargin sun yi cuwa-cuwarsu. To me zai sa shi ba za a tilasta masa bayyana a gaban shari’a ba don ya wanke kansa daga zargin da suka yi masa a gaban alkalai? Ya fi karfin haka ne, ko kuwa shi shafaffe da mai ne?  Ya kamata ke nan a ce  kura na shan bugu gardi kuma na karbe kudi game da shari’ar Sambo Dasuki da Olisa Metuh? 

Idan har za a ci gaba da jan-kafa game da yanke hukunci kan karar da aka kai Kanar Sambo Dasuki, mai ritaya, gaban alkali, to sai a hanzarta bayar da belinsa wanda kundin tsarin mulki ya ba shi, a matsayinsa na dan kasa, domin kuwa zargin da ake yi masa ba irin wanda ba a bayar  da beli ba ne ba.