✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An ciro yarinya da ranta bayan ta kwana 3 da faduwa a rijiya a Jos

Yarinyar ba ta samu wani mummunan rauni ba, illa kujewa da ta yi goshinta, da kuma raunin jiki na rashin kuzari.

Yarinyar mai suna Lydia Azatyom ta bata ne aka kuma shiga neman ta, daga baya sai aka gano ta a cikin wata tsohuwar rijiya da ranta bayan kwanaki 3

Lamarin ya faru ne a unguwar Yashi da ke yankin Tudun Wadan Jos inda hankalin iyayen da kuma makwabtan yarinya mai shekara uku ya tashi na tsawon lokaci.

A cewar wakilinmu Lydia na wasa ne da sauran yara a tsakar gidan, sai kawai aka neme ta aka rasa.

Kasancewar yarinyar bakuwa ce da suka zo da iyayenta daga Jihar Kwara ziyara, hakan ya dada tayar da hankalin jama’a, musamman ’yan uwanta da suka kawo musu ziyarar.

“A rana ta uku da batar yarinyar muna ta nema, sai mijina ya kirami a waya, ya fada min cewa an ga Lydia a cikin wani rami, a wani kango inda ake yin bahaya da zubar da shara

“Mutanen unguwa ne suka taimaka aka fito da yarinyar daga cikin rijiyar a inda aka garzaya da ita Asibitin Filato da ke kusa.

“Yarinyar ba ta samu wani mummunan rauni ba, illa kujewa da ta yi a goshinta, da kuma raunin jiki na rashin kuzari. In ji mahaifiyarta,,” in ji Izang, mahaifiyar Lydia.