Rahotannin da aka wallafa a shafukan sada zumunta na zamani a kasar Vietnam sun bayyana yadda aka yi wa wata ’yar kasar tiyatar ciro tarin wasu duwatsu daga cikin mafitsararta.
Kafofin labarai a kasar sun ruwaito rahoton tiyatar da aka yi wa matar mai shekara 34, bayan fito da ita daga dakin bayar da kulawar gaggawa na Babban Asibitin Phu Binh da ke garin Thay Nguyen.
- Dan shekara 52 ya shiga hannu kan laifin kwanciya da ’yarsa
- Magidancin da ya nemi yada hoton tsiraicin matarsa ya shiga hannu
- Rikicin aure ne matsalar da aka fi kawo wa Hisbah a Kano
Kafin tiyatar ta dade tana koken fama da ciwon ciki inda bayan yi mata wasu gwaje-gwaje da daukar hoton cikin cikin aka gano wasu abubuwa nade a cikin.
An sanya mata rana don yin tiyatar gaggawa inda aka samu duwatsu a dunkule da suka kai tsawon santimita 10 da nauyin giram 400 wadanda aka fitar daga cikin mafitsararta.
Ba a bayar da cikakken bayani game da lamarin ba, sai dai an wallafa hoton cikin matar inda aka tabbatar da wani abu a ciki.
Bayan yin tiyatar an dauki hoton duwatsun da aka samu a dunkule tari guda, wanda hakan ya jefa ma’aikatan asibiti cikin mamakin gaske dangane da abin da aka fitar.
Mujallar Kiwon Lafiya ta Turkish Journal ta shekarar 2014 ta ce, “An taba samun duwatsu a cikin wani mutum da suka kai nauyin giram 100 wanda ya zama bakon abu, kuma an samu faruwar hakan sau 85 a shekarun baya.
Sai dai samun duwatsun da suka kai nauyin giram 400 abin mamaki ne matuka kuma ya shiga cikin tarihi.
Wannan rahoton ya bambanta da irin duwatsun da aka dade ana samu a shekarun baya, inda a shekarar 2016 likitocin China suka fitar da rahoton wani mutum mai shekara 54 da aka fitar wa duwatsun da suka kai nauyin giram 1,048 a cikin mafitsararsa, hakan ya zama duwatsu mafiya yawa da aka taba fitarwa a tarihin kasar China.
An yi ta yada hotunan matar da aka yi wa tiyatar a shafukan sada zumunta na wasu kwanaki a kasar Vietnam, inda wadansu ke ganin a wane irin yanayi take rayuwa da wadannan abubuwa da suke cikinta ga ciwon cikin da take fama da shi.
“Na ji kamar akwai alamar wata kasa a cikina, daga nan na fara jin ciwo.
Yaya matar da take dauke da wannan duwatsu take rayuwa da abubuwan da suke da nauyi?” wani ya tambaya.
Wadansu kuma na mamakin yadda ta jure wa zafin ciwo a cikinta har duwatsun suka taru da yawa haka.