✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

An cimma yarjejeniyar kawo karshen rikicin Tigray

Rikicin ya barke ne a ranar 4 ga Nuwamba, 2020.

Bangarorin da ke yakar juna tsawon shekaru biyu a Habasha (Ethiopiya) sun cimma yarjejeniyar rungumar sulhu don kawo karshen tankiyar da ke tsakaninsu.

An cimma yarjejeniyar ce bayan tattaunawar da Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta shiga tsakani a Afirka ta Kudu.

Jakadan AU na musammam kuma tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Pretoria, babban birnin Afirka ta Kudu.

Obasanjo ya ce Gwamnatin Habasha da wakilan Tigray sun amince da kwance damarar yaki.

Kazalika, sannu a hankali kuma cikin doka da oda za a tsara yadda za a karbi makamai daga hannun mayakan.

Cimma yarjejeniyar sulhu dai wani babban al’amari ne a rikicin na Ethiopiya wanda zai kawo ci gaba a yankin a cewar Obasanjo.

Wannan dai na zuwa ne bayan zaman tattaunawar da ta dauki tsawon mako guda ana laluben hanyar kawo karshen wannan rikici, da ya kashe daruruwa daura da koran dubbai daga matsugunnensu.

’Yan tawayen na Tigray sun yaba da yarjejeniyar kuma sun ce za su mutunta yarjejeniyar da aka kulla.

“A shirye muke mu aiwatar da kuma gaggauta tsagaita wuta karkashin wannan yarjejeniya,” in ji shugaban tawagar ‘yan tawayen Tigray, Getachew Reda.

Rikicin ya barke ne a ranar 4 ga Nuwamba, 2020, lokacin da Fadar Addis Ababa ta aike da sojoji zuwa yankin Tigray bayan da ta zargi kungiyar TPLF, da ke mulkin yankin, da kai hari kan sansanonin sojojinta.