✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ci tarar Yaya Toure Naira miliyan 21 saboda shan giya

A ranar Litinin da ta wuce ne wata kotu a Ingila ta yanke wa dan kwallon kulob din Manchester City da ke Ingila kuma haifaffen…

A ranar Litinin da ta wuce ne wata kotu a Ingila ta yanke wa dan kwallon kulob din Manchester City da ke Ingila kuma haifaffen Kwaddebuwa Yaya Toure tarar Fam dubu 54 kwatankwacin Naira miliyan 21 bayan ta same shi da laifin tuka mota bayan ya sha giya. Sannan kotun ta dage shi daga yin tuki har na tsawon watanni 18 bayan dan kwallon ya amince da laifinsa a kotun.

Yaya Toure, dan kimanin shekara 31 ya amince da laifin yin tuki bayan ya sha giya a gaban kotun da hakan ta sa aka yanke masa hukunci ba tare da bata lokaci ba. Sai dai ya nuna bai san yadda aka yi har ya kwankwadi giya sannan ya tuka mota ba.
Laifi ne a Ingila wani ya yi tuki bayan ya sha giyar da ta wuce kima da hakan ta sa aka zartar wa dan kwallon wannan hukunci don ya zama darasi ga wasu.
Sai dai kocin Manchester City Pep Guardiola a wata hira da aka yi da shi jim kadan bayan kotun ta yanke hukuncin ya ce zai cigaba da sanya Yaya Toure a wasa saboda bai shafi harkar kwallonsa a kulob din ba. “Al’amari ne da ya shafi rayuwarsa ba ta kwallo a kulob din City ba,” inji Guardiola.
Yaya Toure wanda aka shaide shi da kyamar giya, jama’a da dama sun yi mamakin yadda aka samu dan kwallon da laifin shan giya sannan ya yi tuki a wannan lokaci.