✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An ci tarar Kano Pillars miliyan 9 saboda lalata motar Katsina United

Daga yanzu kuma Pillars za ta koma buga wasanninta na gida a Abuja

Hukumar Gudanar da Gasar Firimiyar Najeriya (LMC), ta ci kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars tarar kudi miliyan tara tare da rage mata maki uku kan irin barnar da magoya bayanta suka yi wa kungiyar Katsina United a ranar Asabar.

Hukumar ta dauki wannan mataki ne biyo bayan yadda wasu magoya bayan Pillars din suka yi wa motar daukar ’yan wasan Katsina United kaca-kaca, bayan tashi daga wasan, wanda suka yi kunnen doki.

Hukumar ta sake gargadin Pillars kan sake rage mata maki da zarar aka sake samunta da wani laifi makamancin haka a gaba.

Kazalika, an bai wa Kano Pillars umarnin gyara ko sauya wa Katsina United motarsu da aka lalata.

Sannan an mayar da Pillars da buga wasa daga Kano zuwa a filin wasa na M.K.O Abiola da ke birnin tarayya Abuja.

Kano Pillars da Katsina United za su kammala wasan wanda ba a tashi ba sakamakon tashin-tashina da aka samu a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano, a ranar Litinin a Abuja.

Har wa yau, daga cikin hukuncin da aka yanke wa kungiyar, an hana magoya bayanta halartar wasannin da za ta buga har zuwa karshen kakar wasanni ta bana.

Wasan da Kano Pillars ta buga da Katsina United, shi ne wasa na farko da ta yi a gida cikin shekara biyu tun bayan bullar annobar COVID-19, wanda gwamnatin jihar ta yi amfani da filin wasan a matsayin wurin killace masu cutar.

%d bloggers like this: