✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An ceto yarinyar da aka sayar N100,000 a Kaduna

An ceto yarinyar ce bayan an sayar da ita

An ceto wata yarinya ’yar shekara shida wadda aka sace aka kuma sayar da ita N100,000 a Jihar Kaduna.

Rundunar ’yan sandan jihar ta ce bayan samun rahoton bacewar yarinyar ranar 23 ga Janairu, jami’anta suka sunkuya bincike wanda a karshe aka kama wata makwabciya da ake zargi da hannu a bacewar ’yar.

“A halin bincike an sake kama wani mutum da wata mata da suke da hannu a bacewar yarinyar,” in ji rundunar.

Ta kara da cewa an kubutar da yarinyar ce ba tare da wani rauni ba bayan kuma an sayar da ita a kan N100,000.

Tuni dai aka sake hada yarinyar da iyayenta.