Akalla ’yan Afirka 150 masu yunkurin tsallakawa Nahiyar Turai domin ci-rani ne aka ceto a gabar ruwar tsibirin Canary dake kasar Spain bayan kwale-kwalensu uku sun kife a ranar Alhamis.
Kungiyar ceto ta Salvamento Maritimo dake kasar ta wallafa a shafinta na Twitter cewa an ceto ’yan ci-ranin ne zuwa bakin gaba domin a ci gaba da ba su kulawa.
Adadin mutanen da suke kantafi da rayuwarsu a kokarin tsallakawa Turai dai a bana ya tashi matuka.
Wasu alkaluma daga Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya sun ce akalla mutane 22,249 ne suka yi kokarin tsallakawa nahiyar ta barauniyar hanya, sabanin 2,700 kacal din da aka samu a bara.
Ba za a iya tantance adadin wadanda suka rasu a kokarin tsallakawar ba, sai dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutanen da suka rasu za su iya haura 400.
Tsibirin Canary dai na da iyaka da Tekun Atlantic mai nisan kimanin kilomita 100 daga gabar Afirka ta Yamma.