Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce sojojin sun ceto mutum tara daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Lahadi da yamma.
Gwamnatin jihar a cikin wata sanarwa ta ce ta samu bayanin hakan ne daga hedikwatar tsaro ta Operation Thunder Strike (OPTS).
- Masu garkuwa sun sako dalibai da malamarsu a Kaduna
- An yi garkuwa da uwa da ’ya’yanta hudu a Kaduna
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane a Abuja
- An yi garkuwa da amarya a hanyar gidan miji
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan, ya ce, “Sojojin Operation Thunder Strike da ke sintiri na yau da kullum ne suka samun kiran neman agajin gaggawa”.
’Yan bindigar da ke dauke da makamai sun bude wuta a kan wata motar bas, suka kashe direbanta nan take.
Lokacin da suka isa wurin, ’yan bindigar sun riga sun sace mutum tara daga motar bas din mai kujera 18 mai lambar Kaduna MKA-151.
Nan take sojojin suka kai dauki tare da tseratar da wanda aka yi garkuwa da su baki daya.
“Nan take sojojin suka bi sawun ‘yan bindigar suka yi musayar wata da su har suka kubutar da daukacin mutum taran da aka yi garkuwa da su”, inji Aruwan.
Abin takaici, direban da fasinjan da ke gaban motar bas din sun rasa rayukansu.
Gwamnatin Kaduna ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan wanda suka rasa rayukan nasu yayin garkuwar.
Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da sanar da al’umma dukkan wasu bayanai da suka shafi harkar tsaron jihar, musamman abin da ya shafi garkuwa da mutane.
Ta kara da cewa zata ci gaba da tabbatar da ingancin harkar tsaro ta hanyar hadin guiwa da Gwamnatin Tarayya, wajen kawo karshen matsalar garkuwa da mutane a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Aruwan ya kuma ce jihar na aiki kafada da kafada da jihohin Zamfara da Katsina da Neja da Nasarawa da Filato da Sakkwato da kuma Kano da sauran jami’an tsaro wajen ganin an kakkabe bata-garin da suka addabi yankin.