✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto mutum 36 da aka yi garkuwa da su a Sakkwato

Jami'an tsaro sun ceto wasu mutane 36 da aka yi garkuwa da su daga hannun ’yan ta'adda a Jihar Sakkwato.

Jami’an tsaro sun ceto wasu mutane 36 da aka yi garkuwa da su daga hannun ’yan ta’adda a Jihar Sakkwato.

A ranar Litinin ne haɗin gwiwar jami’an tsaron suka kuɓutar da mutanen da aka sace daga sassan jihohi Zamfara da Sakkwato aka ɓoye su a Dajin Ditibali da ke kan hanyar Isa-Sabon Birni-Goronyo a Jihar Sakkwato.

Surajo, wani mazaunin yankin Isa, ya shaida wa wakilinmu a ranar Litinin ceto an kawo mutum 36 da gawarwaki biyu.

Ya ce, “mun yi imani cewa jami’an sun kashe ’yan ya’adda masu yana a samamen.”

Mashawarcin gwamnan jihar kan sha’anin tsaro, Kanar Ahmed Usman, ya tabbatar wa wakilinmu cewa jami’an tsaro sun kai farmakin, amma ba a ba shi rahoton sakamakon aikin ba tukuna.

Ya ce, “Muna sane da aikin domin gwamnatin jihar ce ta ɗauki nauyinsa, kuma haɗin gwiwa ne na hukumomin tsaro daban-daban da ke Jihar Sakkwato, ciki har da ’yan Banks da jami’an tsaron al’umma. Ranar Litinin aka yi aikin kuma na tabbata an yi nasara, amma dai ina jiran rahoto tukuna,” in ji shi.