✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka da aka sace

'Yan sandan sun yi nasarar ceto ma'aikatan biyu da aka sace.

‘Yan sanda sun ceto ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka biyu da aka sace a Jihar Anambra.

Sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ikenga Tochukwu, ya fitar ranar Juma’a, ta ce “da sanyin safiyar yau, 19 ga watan Mayun 2023, gamayyar jami’an tsaro ta ceto sauran mutum biyu da aka sace lokacin da aka kai hari kan ayarin motocin ofishin jakadancin Amurka” a Jihar Anambra.

Ya kara da cewa babu abin da ya samu mutanen da aka kubutar.

A cewarsa, ‘yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike kuma zai sanar da manema labarai da zarar an samu karin bayani kan maharan.

Akalla mutum hudu aka kashe a harin da aka kai wa ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka a kan hanyar Atani zuwa Osamale a Jihar Anambra.

Tun da farko, DSP Tochukwu ya shaida wa Aminiya cewa “Maharan sun kashe jami’an ‘yan sanda biyu da wasu ma’aikatan ofishin jakadancin biyu, suka kuma cinna wa gawarwakinsu da motarsu wuta.

“Ko da maharan suka ga ’yan sanda na zuwa wurin, sai suka yi garkuwa da ’yan sanda biyu da direban mota ta biyun inda suka gudu. Babu wani dan kasar Amurka a cikin motocin,” in ji shi.