✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An ceto jaririyar da mahaifiyarta ta jefa a masai a Kano

Wata mata ta jefa jariyarta a masai a unguwar Sabon Titi Gidan Kankara da ke Karamar Hukumar Birini a Jihar Kano. Yayar jaririryar mai shekaru…

Wata mata ta jefa jariyarta a masai a unguwar Sabon Titi Gidan Kankara da ke Karamar Hukumar Birini a Jihar Kano.

Yayar jaririryar mai shekaru shida ce ta ruga makwabta ta sanar da su abin da mahaifiyar tasu mai larurar kwakwalwa ta aikata, inda suka kira hukumar kwana-kwana don ganin an ceto jaririyar.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce makwabtan ne suka kira hukumar don ganin an ceto jaririyar kuma an yi nasarar ceto da ranta.

Ya ce bayan samun kiran ne hukumar ta tura tawagar bada agajin gaggawa, kuma “Alhamdulillah an ceto jariryar kuma mun kai wa kakaknta mai suna Abunakar Umar Usman da suke unguwa daya.”

Jami’in  ya ce hukumar ta samun labarin cewa shekarun mahaifiar jaririar 25 kuma aurenta ya dade da mutuwa.