An ceto Manjo Christopher Dantong, hafsan sojin da ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi a makarantar horas da kananan hafsoshin soji ta NDA.
Hadin gwiwar sojoji da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da sauran hukumomin tsaro ne suka kubutar da Manjo Dantong, a ranar Alhamis, 17 ga Satumba, 2021, bayan sun kashe ’yan bindiga sun kuma tarwatsa sansanoninsu a yankin Afaka zuwa Birnin Gwari na Jihar Kaduna.
- Mu da ma’aikatan gwamnati ba mai son a magance matsalar tsaro —Dan bindiga
- Halin da ’yan bindiga ke ciki bayan katse hanyoyin sadarwa
Da yake tabbatar da hakan, Daraktan Yada Labaran Runduna ta 1 ta Sojin Kasa ta Najeriya, Kanar Ezindu Idimah, ya ce tuni aka kai Manjo Dantong zuwa NDA bayan ya samu kulawa daga wani rauni da ya samu.
A cewarsa, za su ci gaba da share yankin har sai sun kamo wadanda suka kashe hafsoshin domin su fuskanci hukunci.
A ranar 24 ga watan Agusta, 2021 ’yan bindiga suka saci jiki suka kutsa cikin harabar NDA da ke yankin Afaka a Jihar Kaduna, inda suka kashe wasu hafsoshin soji biyu, suka kuma yi awon gaba da Manjo Dantong.