✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An ceto daruruwan mutane a jirgin ruwa da ya kama wuta

An ceto fasinjojin jirgin baki daya ba tare da wani ya jikkata ba.

An ceto daruruwan mutane daga wani jirgin ruwa da ya taso daga kasar Girka zuwa Italiya wanda da ya kama wuta.

Sai dai hukumomi sun ce  ba a  samu rahoton mace-mace ko jikkata ba.

Jirgin ruwan na wani kamfani mai suna Euroferry Olympia mai dauke da tutar Italiya ya taso ne daga Igoumenitsa, tashar ruwa mafi girma a yammacin Girka, inda ya nufi tashar ruwan Brindisi dake Italiya, amma sa’o’i kadan da tashinsa ya kama da wuta.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Juma’a, kuma jami’an tsaron gabar teku sun ce fasinjoji 237 da ma’aikatan jirgin 51 ne a cikin jirgin lokacin da wutar ta tashi.

An dai aike da kwale-kwalen ceto don tseratar da rayuwar mutanen, kamar yadda kyaftin din jirgin ya bayyana.

An yi nasarar ceto dukkanin fasinjojin kuma suna cikin koshin lafiya, kamar yadda Sakataren Harkokin Wajen Girka, Kostas Katsafados, ya shaida wa gidan rediyon Skai.

Wani faifan bidiyo da aka dora a shafin intanet na kamfanin dillacin labaran Girka (Proto Thema), ya nuna wani jirgin ruwa da ya kama da wuta, yayin da hayaki mai tarin yawa ya turnuke cikin jirgin.

An kai fasinjojin da ma’aikatan jirgin, wadanda aka kwashe a cikin kwale-kwale, zuwa tsibirin Corfu, inda aka ba su agajin gaggawa, in ji hukumomi.

%d bloggers like this: