✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An caka wa saurayi wuka a Kano

Wani matashi ya daba wa abokinsa wuka a yayin wata takaddama a Kano.

Wani matashi ya daba wa abokin karawarsa mai suna Abubakar Sani wuka a ya aika shi lahira saboda wata takaddama a Jihar Kano.

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta ce matasan cikin sa-in-sa, sai wanda ake zargin ya zaro wuka ya luma wa Abubakar a ciki a unguwar Sharifai da ke Karamar Hukumar Ungogo.

Kakakin Rundunar, DSP Abdullahi Haruna, ya ce, “Mun samu rahoto cewa ya daba wa Abubakar wuka da misalin karfe 7 na daren ranar 7 ga watan Afrilu, 2021.

“Da muka isa wurin sai aka garzaya da wanda aka daba wa wukar Asibitin Kwararru na Murtala da ke Kano, inda aka kwantar da shi.

“A ranar 10 ga wata kuma likitoci suka sanar da mu cewa ya riga mu gidan gaskiya.”

Ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala binciken da Kwamishian ’Yan Sandan Jihar, Sama’ila Dikko, ya ba da umarnin gudanarwa a Sashen Binciken Manyan Laifukan da suka danganci kisan kai.