’Yan sanda sun cafke wani matashi mai shekara 35 kan yi wa kananan yara hudu fyade a rana guda a Karamar Hukumar Biu ta Jihar Borno.
Rahoto rundunar ’yan sandan jihar ya cewa biyu daga cikin kananan yaran ’yan shekara 11 ne sauran biyun kuma ’yan shekaru 12 ne.
- Landan Ta Ci Tarar Saurayi Kan Yi Wa Budurwa Dan Kira Landan
- Masu Hana Zaman Lafiya A Najeriya Ba Za Su Yi Nasara Ba —Buhari
A lokacin da yake wa manema labarai bayani a hedikwatar ’yan sanda jihar, matashin ya yi ikirarin yi wa kananan yaran fyade ya ba su N20o kowaccensu, ya kuma roki hukumomi su yi mishi sassauci.
’Yan Sandan Jihar Borno, CP Abdu Umar, ya ce matashin wanda ke sana’ar dinki a garin Biu ya fara yaudarar ’yan mata biyu zuwa cikin shagonsa da safe ya yi lalata da su, ya basu N200 kowaccensu.
A ranar ne suka tura wasu kawayensu biyu ’yan shekara 12, zuwa shagonsa, ya yi lalata da su, ya ba su kudi kamar na farkon, kafin daga baya iyayen ’yan matan su kai wa ‘yan sanda rahoto.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Borno, CP Abdu Umar, ya shaida wa maneman labarai cewa an samu laifuka 102 na fyade a shekarar 2022 da ke karewa.
Ya ce an samu karuwan yi wa kananan yara mata fyade a jihar duk da kokarin masu fada a ji wajen yakar matsalar; amma a halin yanzu ana samun karin nasarori wajen shawo kan matsalar.
Amma “Ba na jin akwai wata shari’a ta fyade da za ta zo nan ba tare da mun gurfanar da masu laifin ba gaban kuliya ba,” in ji shi.
CP Umar ya ce baya ga gurfanar da masu fyade a gaban kotu akwai masu aikata sauran laifuka da ta gurfanar a gaban kotu kun an yanke musu hukunci.
Ya kara da cewa, “Har yanzu muna da wasu da ake zargi da aikata laifuffuka da dama da za su fuskanci kuliya.”
A halin da ake ciki, ’yan sanda sun samu rahoon laifuka 500 ciki har da kisan kai, fashi da makami 22, garkuwa da mutane 30, fyade 11, ta’ammali da kwaya 28 da na sata 138.
Laifukan bakwai da suka shafi na siyasa na mutane 12 da ake zargi daga APC da wasu 2 da ake zargi daga PDP na tada hankali yayin yakin neman zaben.