Rundunar ‘yan sandan Kano ta cafke wasu mutum 3 da ake zargi da kisan Alhaji Kabiru Ya’u da ‘yarsa Harira Kabiru.
Kakakin ‘yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce a ranar 26 ga watan Agusta 2020 wadansu mutane, sun haura gidan Alhaji Kabiru Ya’u suka kashe shi tare da diyarsa a kauyen Gomo da ke karamar hukumar Sumaila a Jihar Kano.
- ’Yan bindiga sun kai hari a Kano
- Gwamnatin Kano ta yi wa ‘yan jarida bita kan cutar Coronavirus
- Abin da ya sa na tube Sanusi daga Sarautar Kano —Ganduje
Haruna Kiyawa ya ce, “Bayan samun rahoton, Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar Kano, Habu A. Sani, nan da nan ya tashi rundunar ‘Operation Puff Adder’ karkashin jagorancin DSP Shehu Dahiru da su kamo masu laifin.
“Tawagar nan take ta fara aiki, wanda a ranar 19 ga Disamba, 2020, ta cafke Adamu Musa, Sule Mallam, da Isyaku Sule.
Ya ce bayan bincike, an gano dukkan wadanda ake zargin suna da adireshi iri daya kuma makwabta ne ga mamacin.
Bayan gudanar da bincike, makwabcin nasa, ya amsa cewa shi ya umarci ‘ya’yansa uku da jikansa daya da su kashe yarinyar saboda tana zargin yana garkuwa da mutane.
Wanda ake zargin sun amsa cewa sun yi amfani da adda da sanduna wajen kashe mamacin da diyarsa.
Sanarwar ta bayyana cewa za a ci gaba da gudanar da bincike domin kamo ragowar wanda suke da hannu a kisan tare da gurfanar da su gaban kotu.