✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke matashi kan zargin asiri da sassan jikin mutane a Bauchi

Wanda ake zargin ya amsa cewa ya yi hakan ne don yin asirin kudi.

‘Yan sanda a jihar Bauchi sun cafke wani matashi mai shekaru 22 a duniya, bisa zargin cire sassan jikin wani matashi a Karamar Hukumar Alkaleri.

Kakakin ‘Yan Sandan jihar, Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin.

Ya ce, “A ranar 21 ga Disamban 2020, mun cafke wani mutum mai shekaru 22 dake kauyen Unguwar Alkaleri, wanda ake zargi da kashe Adamu Ibrahim, mai shekaru 17.

“Ya cire masa idanu, ya kuma kone wasu sassa na jikinsa, sannan ya binne shi a wani rami.

“Yayin bincikarsa, an sami wasu sassan jikin mamacin da ya kashe, an dauke su zuwa babban asibitin Alkaleri don yin bincike.

“Likita a asibitin ya tabbatar da cewa an cire wasu sassa na jikin matashin da aka kashe,” inji Ahmed.

Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, inda yace ya cire idon nasa ne don zai yi asirin samun kudi.

Kazalika, ‘yan sandan sun ce an sami karamar wuka a jikinsa, ashanar kunna sigari, da kuma talkami.

Kakakin ‘yan sandan ya ce za a ci gaba da bincike kafin daga bisani su mika shi kotu don ya girbi abinda ya shuka.