‘Yan sanda a Jihar Legas sun damke tare da gurfanar da wasu mutum shida a kotu bisa zargin satar kayan kida a coci wadanda aka kiyasta kudinsu ya kai Naira miliyan 28.
An ce matasan da aka gurfanar a gaban kotun majistare da ke Yaba, sun fasa cocin ne sannan suka shiga suka wawushe kayan kidan da ake amfani da su wajen gabatar da ibada.
- An dage sauraron karar Hadiza Gabon saboda rashin lafiyar matar alkali
- Najeriya na kan gaba wajen noma da shan Tabar Wiwi a duniya — NDLEA
Wadanda aka kama din su ne Kelechi Israel da James Abichele da Simon Abi da Ifeanyi Mba da John Odiong da kuma Austin Bassey, dukkansu ‘yan tsakanin shekara 25 zuwa 47.
Ana zarginsu ne da aikata laifuka hudu da suka hada da hadin baki da fasa wurin ibada da sata a killataccen wuri da kuma shiga wuri ta haramtacciyar hanya.
Sai dai baki dayansu sun musunta aikata ko daya daga cikin wadannan laifukan.
Tun farko ‘yar sanda mai gabatar da kara, ASP Rita Momah, ta shaida wa kotun cewa wadanda ake zargin sun aikata laifuffukan ne da misalin karfe 11.50 na daren shida ga watan Yunin 2022, a cocin Redeemed Evangelical Mission da ke Gbagada a Jihar Legas.
Ta ce laifukan da suka aikata sun saba wa sashe na 411 da 311 da 340 da na 287 (5) {f} na Dokokin Manyan Laifuka na Jihar Legas na 2015.
Alkalin kotun, Adeola Adedayo, ta ba da belin wadanda ake zargin a kan Naira miliyan shida ga kowannensu tare da shaidu biyu-biyu.
Daga nan, ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar biyu ga Augusta mai zuwa.
(NAN)