Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Oyo ta ce ta cafke wata mata mai kimanin shekaru 24 bisa zargin satar jariri dan wata shida da haihuwa.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Nwachukwu Enwonwu shine ya bayyana hakan ga ‘yan jarida lokacin da yake gabatar da wacce ake zargin a ranar Alhamis.
Ya ce lamarin ya faru ne ranar shida ga watan Satumbar 2020 da misalin karfe tara na dare a unguwar Eleiyele dake Ibadan.
Kwamishinan ya kuma ce wacce ake zargin ta je waurin wata kawarta ce mai gyaran gashi inda ta tarar da wata mata na wasa jaririn makwabciyarta mai kimanin wata shida.
A cewarsa, daga nan ne matar ta karbi yaron da nufin wai tana yi masa wasa kafin daga bisani ta kais hi wani wuri ba tare da sanin mai gyaran gashin ba.
“Jim kadan da samun labarin, jami’anmu suka bazama inda suka cafke wacce ake zargin ranar 24 ga watan Satumba a Ilara-Mokin a jihar Ondo kuma aka ceto yarinyar ba tare da an ji mata ko da kwarzane ba,” inji kwamishinan.
Da take tattaunawa da ‘yan jarida, wacce ake zargin da ta ce ta rabu da mazajen da ta aura a baya har guda uku saboda rashin hannu da shuni ta yi ikirarin cewa ta dauki jaririn ne domin ta raine shi a matsayin dan ta.
Ta ce, “Na zo ne daga Akure domin na gai da kawata wacce ke sana’ar gyaran gashi a Ibadan, sai na ga mahaifiyar a shagon kawar tawa.
“Sai na fara wasa da jaririn kafin ta dawo da bashi nono a lokacin yana kuka.
“Niyya ta ita ce na raine shi am matsayin da na saboda lokacin da muka rabu da miji na a watan Afrilu ina da juna biyu, ni kuma yanzu ba na son mutane su gane ba na dauke da juna biyun,” inji ta.
Daga nan sai ta ce mahaifinta ne ya tilasta mata rabuwa da mazajen nata har uku a baya saboda wai ba su da hannu da shuni kuma ba su dace da ita ba.