✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke mai yi wa EFCC sojan gona

A Jihar Kurosriba, jami’an tsaro na farin kaya sun damke wani mutum a Kalaba babban birnin jihar mai suna Peter Akpanke, bisa zarginsa da yi…

A Jihar Kurosriba, jami’an tsaro na farin kaya sun damke wani mutum a Kalaba babban birnin jihar mai suna Peter Akpanke, bisa zarginsa da yi wa hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) sojan gona, inda yake bayyana kansa a matsayin jami’in hukumar.
Bayan Akpanke da ya shiga hannu, akwai karin wasu matasa biyu, Rufus Awu da Charles Ikpeme, su kuma da suka rika yawata gari suna cewa su jami’an hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ce ta Jihar Kurosriba (CTRA), alhalin karya ce tsagwaronta suke sharawa.
Aminiya ta samu bayanin cewa matasan biyu an cafke su ne a wani otel, yayin da ake zarginsu da kitsa yadda za su damfari wani babban ma’aikacin gwamnati a jihar; Naira milyan goma. Haka kuma ana zargin su ne suke hada baki da Peter Akpanke, da ya fito a matsayin jami’in hukumar EFCC.
Mai magana da yawun hukumar tsaro ta DSS, Betina Ogoro da wakilinmu ya tuntube ta, bat a ce uffan ba game da lamarin amma wata majiya kusa da ofishin ta tabbatar da cewa lamarin ya faru kuma shi Akpanke, tsohon ma’aikacin hukumar EFCC ne, wanda hukumar tad ade da korarsa, shi da wani mai suna Kabiru Shehu Bala.