✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke kananan yara 5 kan ayyukan matsafa a Kwara

An kwace makamai da miyagun kwayoyi da kuma ganye da ake zargin tabar wiwi ce a hannun kananan yaran

’Yan sanda sun tsare wasu kananan yara maza uku da mata biyu kan zargin ayyukan kungiyar matsafa da kuma sace-sace a  Jihar Kwara.

Kakakin ’yan sandan jihar, Ajayi Okasanmi, ya ce, “An kwace makamai da miyagun kwayoyi da kuma ganye da ake zargin tabar wiwi ce a hannun kananan yaran.” 

Ya ce dubun kananan yaran ta cika ne a ranar 26 ga watan Afrilu a wata matattarar bata-gari da ke yankin Gambari/Oja Gboro.

Ya ce, “Bayan samun bayananan sirri jami’anmu suka kai samame a dabar da ke kusa da Kokewu-Kobere a unguwar Oja Gboro, inda su aka kama su biyar din.”

Ya ce an gano yaran mambobin wata kungiyar asiri ce da ke addabar jama’a suna kwace musu kayayyaki a yankin.