✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke dan sanda da satar waya da kudi a Osun

Olayiwola ya saci wata wayar salula ta Ajiboye kirar Techno Camon 12 wadda darajarta ta kai Naira dubu 58.

An kori wani jami’in dan sanda, Felix Olayiwola, da aka gurfanar a gaban Kuliya da laifin satar wayar hannu da kuma kudi har naira dubu 25 na wani matashi, Bolaji Ajiboye a Osogbo, babban birnin jihar Osun.

Jami’in dan sanda da ya shigar da kara a gaban kotun, Idoko John, ya bayar da shaidar cewa mutumin da ake zargi ya aikata laifin wanda yana cin karo da sashe na 390 cikin dokokin miyagun laifuka na jihar Osun da aka kaddamar a shekarar 2002.

An ba da shaidar cewa Olayiwola ya saci wata wayar salula ta Ajiboye kirar Techno Camon 12 wadda darajarta ta kai Naira dubu 58, lamarin da ya sanya aka kama shi tare da tsare shi a ofishin ‘yan sanda da ke Osogbo.

Bayan sallamarsa daga aiki ne aka gurfanar da shi a gaban wata Kotun Majistire da laifin dan hali, inda bayan bayar da belinsa a kan Naira dubu 100, Mai Shari’a Ope Oladele ta dage sauraron karar zuwa ranar 9 ga watan Nuwamban 2020.