Rundunar tsaro ta hadin gwiwa a Kuros Riba da ake kira Akpakwu, ta cafke wani barasarake a kauyen Ikot Atambi da ke Karamar Hukumar Akpabuyo a jihar kan zargin garkuwa da mutane.
An cafke Etiyin Atambi Eyo tare da matarsa da kuma dansa bisa zargin su da satar mutane da neman kudin fansa.
- Surutai ba za su sa mu tattauna da ’yan bindiga ba —El-Rufai
- Majalisa ta nemi Buhari ya ayyana dokar ta-baci a Najeriya
Alfred Mboto Babban Jami’i mai ba gwamnan Jihar shawara kan harkokin tsaro ya tabbatar wa Aminiya cewa, “Hakika basaraken da ake zargi ya shiga hannu.
“Ya amsa laifinsa da cewa shi da matarsa da dansa ne suke kama mutane suna garkuwa da su.
“Kazalika, mataimakina ya tabbatar da cewa an rusa gidansa da ke Kalaba, babban birnin jihar,” in ji Alfred.
Bayanan da Aminiya ta samu sun nuna cewa, Atambi yana da wani tsafaffen wuri da yake girke mutanen da aka farauto masa a matsayin garkuwa.
Dubun Basaraken ta cika ne a ranar Talata bayan da aka tsegunta wa jami’an tsaro su Kuma suka kai samame suka kama su.
Karamar Hukumar Akpabuyo ta yi kaurin suna a matsayin maboyar masu sata da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.