Sarkin Samarin Masarautar Jama’a da ke karamar hukumar Jama’a a jihar Kaduna, Alhaji Mudi Shafi’u Tahir, ya yi kira ga gwamnati a kowane mataki da su kara himma wajen saukakawa jama’arsu halin kuncin rayuwar da suke ciki a sakamakon yanayin da suka tsinci kansu.
Hakan nada nasaba ne da hauhawar farashin kayayyaki a daidai lokacin da suke kiyaye dokar zaman gida da gwamnatoci suka sanya don dakile cutar Covid-19 da ta addabi duniya.
Sarkin Samarin, ya ce a daidai irin wannan lokaci da gwamnatoci suka tunkari yaki da cutar coronavirus, to wajibi ne su kula da hakkin jama’a musamman talakawa da sauran mabukata.
Sarkin, ya yi wannan kiran ne jim kadan bayan kammala rabon kayayyakin abinci da suka hada da: Buhunan shinkafa da taliya da man gyada a garin Kafanchan.
“Wannan tallafin na yi shi ne tsakani da Allah lura da irin halin da al’umma ke ciki. Zan yi kira kuma ga kungiyoyi da sauran masu hannu da shuni da ke wannan masarauta da Kudancin Kaduna da ma kasar baki daya da su tashi tsaye don taimakawa mabukatan da ke kusa da su domin ba komai ne sai an jira tallafin gwamnati ba.” Inji shi
A karshe ya shawarci jama’a da su ci gaba da hakuri tare da kiyaye dokar gwamnati da kuma shawarwarin jami’an kiwon lafiya don taimakawa wajen shawo kan matsalar cikin kankanin lokaci maimakon yaduwar da cutar ke ciki gaba da yi a kullum.