✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bukaci gwamnati su bullo da shirin tallafa wa masu fasaha

An yi kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi su bullo da wani shiri da zai rika tallafa wa ’yan kasar nan da suke da…

An yi kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi su bullo da wani shiri da zai rika tallafa wa ’yan kasar nan da suke da fasahar kirkira don bunkasa kasuwanci da tattalin arziki.
Shugaban Cibiyar kirkira Mai Zaman Kanta, Mista Abanka Musa ne ya bayyana haka  lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a wurin bikin karrama ’yan Najeriya da suka kirkiro na’urori da injuna iri-iri da aka gudanar a Abuja a farkon makon nan.
Mista Abanka Musa ya bayyana cewa yin haka shi zai bunkasa kasuwanci tare da tallafa wa tattalin arzikin kasar nan.
“Muddin Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi za su rika karramawa tare da tallafa wa wadanda suka kirkiro wata fasaha to, babu shakka tattalin arzikin kasar nan zai bunkasa kuma su ma kansu wadanda suke yin kere-kere za su samu kwarin gwiwar kara kirkiro sababbin fasahohi,” inji shi.
Daga nan, ya bayyana takaicinsa kan yadda gwamnatoci suke watsi da wadanda suke da fasahar kimiyya da kere-kere, inda ya ce da yawa daga cikin masu fasaha gwiwarsu ta yi sanyi sun yi watsi da kirkiro wata fasaha da za ta bunkasa tattalin arzikin kasa.
Ya bayyana cewa makasudin shirya taron shi ne su tallata ’yan kasa da suke da fasahar kere-kere da kuma irin na’urorin da suka kirkiro.
“Babu shakka wannan biki zai fito da wadanda suke da fasahar kimiyya da kere-kere maza da mata domin duniya ta san su tare da kara musu kwarin gwiwa su ci gaba da bincike da kirkire-kirkire don bunkasa kayayyakin gida,” inji.
Ya ce ta haka ne sauran kasashe suka bunkasa har suka kai matsayin da suke a yanzu.
Mista Musa ya ce sun gayyato mutane daga sassa da dama na kasar nan domin baje-kolin fasaharsu da kirkirar da suka yi don duniya ta gani.
Ya ce hakan zai sanya a gano ’yan kasa da suke da kokari tare da nacin bincike kan kimiyya da kere-kere. Ya ce akwai ’yan Najeriya da yawa da suka kirkiro na’urori iri-iri masu ban mamaki wadanda duniya ba ta san da su ba.
Kuma ya kara da cewa akwai wadanda suka fadadawa tare da kera wata fasaha a kan wacce ake da ita a sauran kasashe. “Muna da mutane daban-daban da muka zakulo wadanda suka kirkiro na’urori masu ban mamaki wadanda ba a taba kera su ba a wata kasa. Kuma akwai wadanda muka gano sun kara fadada fasahar da wata kasa ta yi. Wannan abin mamaki ne,” inji shi.
Ya ce akwai wadanda suka kirkiro motoci da jiragen sama manya da kanana da taraktocin noma da motocin daukar kaya da makamantansu. Sai ya yi kira ga gwamnatoci da masu hannu da shuni su rika tallafa wa fannin kere-kere da fasaha domin bunkasa kasuwanci da tattalin arzikin Najeriya.