✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bukaci a hukunta matar da ta kashe mijinta a Kano

’Yan uwa da iyalan marigayi Malam Ado Ali da ke Unguwar Dorayi a Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano, da ake zargin matarsa mai suna…

’Yan uwa da iyalan marigayi Malam Ado Ali da ke Unguwar Dorayi a Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano, da ake zargin matarsa mai suna Rashida Sa’idu Mohammed ta kashe shi ta hanyar tunkudo shi daga bene sun ce ba su yafe jinin dan uwansu ba, don haka suka yi kira ga hukumomin da abin ya shafa su gaggauta daukar hukuncin da ya dace a kan wacce ake zargi da aikata kisan.

Binciken Aminiya ya gano cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin da ta gabata da misalin karfe 8:00 na dare, lokacin da Rashida Sa’idu ta ji yana yin waya da wata mace da take zargin budurwarsa ce a dakinsa. Hakan ya sa ta yi kokarin kwace wayar daga hannunsa, inda kuma kokawa ta kaure a tsakaninsu har ya samu ya fito daga dakin zuwa barandar benen da suke, ita kuma kishi ya ingiza ta ta tunkudo shi kasa. Nan take ya fado kansa ya fashe, kuma ya karye a wuyansa.

Bayan da lamarin ya auku ne aka garzaya da marigayin, wanda malami ne  a Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Kano zuwa Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, inda aka tabbatar da rasuwarsa.

Benen da ake zargin matar ta tunkuxo marigayin

Binciken Aminiya ya gano cewa ba kawai rigima a kan yin wayar da marigayin ya yi da budurwarsa ba ce, domin wata majiya ta ce an dauki kimanin mako guda ana zaman doya da manja a tsakanin ma’auratan; inda wacce ake zargin ta zargi marigayin da rashin tabbatar da adalci a tsakaninta da uwargidanta a lokacin da ya saya wa ’ya’yansu gwanjo. “Ita da uwargidan sun nemi marigayin ya saya wa ’ya’yansu da suke goyo kayan gwanjo, lokacin da ya kawo kayan sai ya dauki wata riga guda daya ya ba ’yar uwargidan wacce ta yaye. To, hakan da ya yi bai yi wa wacce ake zargin dadi ba, don haka suka fara rigima a tsakaninsu a kan hakan har kara ta kai ga kanen marigayin cewa mijinsu ba ya yi mata adalci, ya fi son uwargidan da ’ya’yanta,” inji majiyarmu.

Safiyya Ado ita ce babba a cikin ’ya’yan marigayin takwas. Ta bayyana wa Aminiya cewa a matsayinsu na ’ya’yan marigayin suna bin kadin jinin mahaifinsu don haka suna neman a zartar wa matar mahaifin nasu hukunci daidai da abin da ta aikata. “Muna neman a yi mana adalci, a yi mata hukuci daidai da laifin da ta aikata domin mu ta cuce mu, ta kashe mana mahaifi. Mahaifinmu mai sonmu, mai daukar nauyinmu. Mai burin ya ga mun yi karatu. Babu abin da za mu ce sai dai mu yi masa fatan samun rahamar Allah,” inji ta.

Malama A’isha Mu’azu ita ce uwargidan marigayin. Ta shaida wa Aminiya cewa “Kafin ta kai ga aikata wannan abu sai da ta sauko daga bene ta same ni ta gaya min cewa wai ta ji maigidanmu yana waya da budurwa yana gaya mata kalaman soyayya. Ni kuma sai na ba ta hakuri na ce ta kyale shi wata rana sai labari. Amma da yake abin ya zo da haka ba ta dauki shawarata ba. Ni dai ban san abin da ke faruwa ba sai jin karar fadowar abu na yi daga sama, kafin in fito daga daki sai ga yara sun shigo da gudu suna cewa abbansu ya fado daga sama. Nan da nan na fito na gan shi kwance cikin jini.”

Malama A’isha ta bayyana mijinta a matsayin mutum nagari wanda yake daukar nauyin iyalansa yadda ya kamata. “Mutum ne mai so tare da kula da iyalansa. Samun mutane masu halinsa abu ne mai wuya. Babu abin da zan ce sai dai in yi masa addu’ar Allah Ya jikansa”, inji ta.

Sai dai wacce ake zargin wacce kuma take da ’ya’ya biyu tare da marigayin, Rashida Sa’idu ta musanta zargin, inda ta ce: “Abin da ya  faru shi ne, na same shi yana waya sai na kai hannuna zan kwace wayar hakan ya sa ya cije ni a hannuna. Sai ya fito daga dakin. Ni ma ban san yadda aka yi ba sai na ji fadowarsa kasa, amma ba ni na tunkudo shi ba kamar yadda ake fadi.”

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, DSP Haruna Abdullahi Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce wacce ake zargin tana hannunsu a sashen binciken manyan laifuffuka na rundunar kuma da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da ita gaban kotu.