A ranar Litinin ce aka yi jana’izar wadansu mutum biyu, Ibrahim Manzo mai shekara 76 da Barnabas Musa, mai shekara 45 da wadansu ’yan bindiga suka kashe a kauyen Ambe Madaki da ke masarautar Numana a Karamar Hukumar Sanga a Jihar Kaduna.
Mutanen, kamar yadda majiyar Aminiya ta ce an kashe su ne ta harbin bindiga a ranar Lahadi da misalin karfe goma na dare a gidansu.
“Abin da ya fi ba mu mamaki shi ne gidan kawai suka tunkara inda suka kashe mutum biyu da suka tarar a ciki ba tare da sun taba kowa ba kuma ba su kona gidan ko su dauki wani abu a ciki ba,” inji majiyarmu.
An gudanar da jana’izar ce a karkashin kulawar sojoji da sibil difens da sauran manyan garin.
Karamar Hukumar Sanga tana daya daga cikin kananan hukumomin da ake yawan samun kashe-kashe a Kudancin Kaduna inda ta kasance daya daga cikin kananan hukumomi hudu da ke karkashin kulawar rundunar tsaron tabbatar da zaman lafiya ta ‘Operation Sabe Haben’ da ke da hedkwata a Jos, Jihar Filato.