✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

An binne gawarwakin mutum 71 da ’yan bindiga suka kashe a Katsina

Mun samu nasarar hallaka akalla ’yan bindiga 100.

An binne gawarwakin mutum 71 da ’yan bindiga suka kashe a wasu kauyuka bakwai na Karamar Hukumar Bakori da ke Jihar Katsina.

Aminiya ta ruwaito yadda ’yan bindiga a ranar Asabar suka kai hari kauyuka bakwai na Karamar Hukumar inda suka hallaka ’yan sa-kai da mazauna fiye da 73.

Kauyukan da lamarin ya shafa sun hada da Jargaba, Gidan Gago, Gidan Alhaji Audu Gari, Gidan Shirai, Gidan Baushe, Unguwar Gogai da Dicika da ke Karamar Hukumar Bakori.

Wadanda lamarin ya rusta da su sun yi artabu da ’yan bindigar yayin da suka fita karbo dabbobinsu da ’yan bindigar suka sace musu.

Mummunan artabun da har yanzu ba a kammala tattara adadin wadanda suka rasu ba, ya auku ne a kauyukan Gidan Gwanki da Gidan Damo da ke Karamar Hukumar Kankara.

Kananan hukumomin biyu dai na fama da hare-haren ’yan bindiga, da satar mutane da shanu da sauran miyagun laifuka.

Guda daga cikin ’yan sa-kan da ya nemi a sakaya sunansa ya ce sun samu nasarar hallaka akalla ’yan bindiga 100, amma ba su da masaniyar guda nawa aka kashe musu.

Wani da ya rasa dan uwansa yayin artabun mai suna Abdullahi ya ce suna cikin alhini.

“Mun saduda, mun sallama cewa wadanda ya kamata su kare rayukanmu ba za su yi ba, domin sun zuba ido ana kashe mu, ya rage namu mu kare kanmu,” in ji shi.

Ya ce dan uwan nasa ya rasu ya bar mata da ’ya’ya, wanda ya ce nauyi ne mai girma da dan uwan nasu ya tafi ya bari a kansu.

Ita ma wata mata da ta rasa danta Usman mai shekaru 25, da matarsa da kananan yara ta ce Allah Ya riga ya rubuta lokacinsa ya yi, amma wannan ba zai hana su ci gaba da kare kansu ba.

Kazalika wani mazaunin Yargoje ya ce bayan artabun farko, ’yan bindigar sun koma karo mayaka, kuma kan hanya ne suka tsaya a wani kauye mai suna Dan Kumaji, inda suka sace mata 27, suka kuma kora dabbobin mutane da dama.

“Mun samu labarin wasu dabbobin daga baya sun dawo gida, amma matan har yanzu suna hannunsu.”

A bangere guda, Kakakin rundunar ’yan sandan jihar SP Gambo Isah, ya ce ba su samu wani sabon bayani ba kan harin ba ya zuwa yanzu.

Sai dai baya ga Gwamna Aminu Bello Masari da ya aika tawaga karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Muntali Lawal don jajanta wa al’ummar kauyukan, su ma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar sun yi tir da lamarin.

Tawagar Gwamann dai ta yi alkawarin kafa kwamitoci biyu da mutum daya daga kauyukan da lamarin ya faru, don raba kayan tallafi ga iyalan wadanda ’yan bindigar suka kashe.