✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bayyana matsalar da ke haddasa rikicin manoma da makiyaya a Jihar Oyo

Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi ya danganta rikicin manoma da Fulani makiyaya da matsalar rashin fahimtar harshen juna a tsakanin al’ummar Fulani makiyaya da…

Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi ya danganta rikicin manoma da Fulani makiyaya da matsalar rashin fahimtar harshen juna a tsakanin al’ummar Fulani makiyaya da manoma Yarabawa a jihar.

Ya ce sau tari ɗan saɓanin da bai taka kara ya karya ba, shi ke janyo ɓaraka saboda rashin fahimtar yaren ɓangarorin biyu, inda ake samun da yawa daga cikin Fulani makiyaya da ba su fahimtar Yarabanci; hakazalika su ma manoma Yarabawa waɗanda ba su fahimtar Fulatanci. 

“A irin haka ne sai ka ga a kan abin da bai kai ya kawo ba an kai ga samun matsala. Baya ga haka, ɓangarorin biyu ba su da wata matsala a tsakaninsu, don haka ne muke shirya tarurrukan zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin Fulani makiyaya da ’yan uwansu Yarabawa manoma, don inganta kyakkyawar fahimta a tsakanin su,” inji shi.

Gwamanan ya shaida haka ne a yayin taron naɗin sarautar Sarkin Fulani na Oke Ogun, inda ya sami wakilcin Kwamishinan ayyuka da sufuri na Jihar Oyo, Wasiyyu Oladimeji Dauda; wanda ya karanta saƙon gwamnan a lokacin da ya gabatar da muƙala ga taron jama’a; mafiya akasarinsu Fulani da suka halarci taron daga sassa daban-daban na ƙasar nan da ma ƙasashen ƙetare. Ya ce gwamnatin jihar na yin iya bakin ƙoƙarinta na ganin an samu fahimtar juna da daidaito a tsakanin ɓangarorin biyu. “Don haka na halarci wannan taro, domin na isar maku da saƙon zaman lafiya na Gwamna Abiyola Ajimobi. Fatanmu shi ne, duk lokacin da aka samu rashin jituwa, a kai zuciya nesa, a miƙa lamarin ga mahukunta” inji shi. 

A nasa ɓangaran, mataimakin shugaban ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Miyatta Allah na ƙasa, Alhaji Usaini Bosso ya shaida wa Aminiya cewa  babu dauwamammar gaba a tsakanin Fulani makiyaya da manoma, “don ko matarka ce wani lokacin kuna yin sabani, sai dai a duk lokacin da Shaiɗan ya gitta abu mafi alfanu sai a bi hanyar maslaha a warware matsalar” inji shi.

A cewarsa, sarautar Sarkin Fulanin Oke Ogun da babban basaraken yankin ya ba Alhaji Yakubu abun alfahari ne da zai haɗe kan al’ummar Fulanin yankin, ya kuma ɗinke duk wata ɓarakar da ke tsakaninsu, domin mutum ne jajirtacce da ya yi rawar gani a matsayinsa na shugaban ƙungiyar Miyatti Allah na Jihar Oyo; inda ya yi aikin wanzar da zaman lafiya a tsakanin ɓangarorin yarbawa da Fulanin yankin.

A nasa ɓangaren, babban basaraken yankin Dokta Ganiyyu Adekunle Salahu, Aseyin na Lardin Iseyi; ya shaida wa Aminiya cewa ya bai wa Alhaji Yakubu Bello sarautar sarkin Fulanin Oke Ogun ne bisa cancantarsa da aiki tuƙuru da yake yi don ganin an samu tabbatacen zaman lafiya a tsakanin Fulanin makiyaya da manoma Yarabawa a yankin. Ya ce yin haka dama ce da za ta ƙara masa ƙarfin yin aiki tuƙuru kamar yadda ya saba.

Sabon sarkin Fulanin na Oke Ogun, Alhaji Yakubu Bello ya shaida wa Aminiya cewa sarautar za ta ƙara masa ƙwarin gwiwa ne bisa aikin da yake yi a baya. Ya ce yanzu zai samu cikakkiyar damar haɗe kan al’ummar Fulani  da sauran ƙabilun yankin. “Za mu ci gaba da  gudanar da tarurrukan zaman lafiya. Kirana ga al’ummar Fulani, su tsare dukiyoyinsu kuma su bai wa ilimin ’ya’yansu fifiko, na addini da na boko, domin rashin ilimi ɗaya ne daga cikin manyan matsalolinmu. Don haka muddin muna son ci gaba sai mun bai wa ’ya’yanmu ilimi,” inji shi.

A ƙarshe ya gode wa ilahirin jama’arsa, bisa goyon bayan da suke ba shi.

Lardin Oke Ogun gari ne a Arewacin Jihar Oyo, mai tarin albarkar kiwo wanda da ya ƙunshi ƙananan hukumomi 6 na jihar. A nan kuma ne fiye da kaso hamsin bisa ɗari na al’ummar Fulani makiyaya ke yada zango, waɗanda kan zo daga ciki da wajan Najeriya a lokacin rani domin yin kiwon dabobinsu,  baya ga tarin Fulanin da suka yi kaka-gida a yankin,  suka zamo ’yan gari.