A ranar Laraba aka yi gagarumin bikin rufe Gasar Rubutattun Wakokin Hausa da aka gudanar a Jihar Sakkwato.
Sashin Hausa na Jami’ar Usman Danfodiyo ya shirya gasar dangane da matsalar tsaro a Arewacin Najeriya.
Bello Shehu Alkanci daga Jihar Zamfara, shi ya zama na daya a babbar Gasar cikin mutum 30.
Abdullahi Adamu Dukki daga Jihar Kebbi ne ya zo na biyu a gasar.
Sai kuma Aliyu Umar Kafin Hausa daga Jihar Jigawa, ya zo na uku a gasar cikin mutum 30 da suka fafata.
Kasancewar Gasar rukuni-rukuni ce, ga yadda sakamakonta ya kasance:
BABBAR GASA
1. Bello Shehu Alkanci (Zamfara)
2. Abdullahi Adamu Dukki (Kabi)
3. Aliyu Umar (Jigawa)
GASAR GA-NI-GA-KA
1. Bashir Malami Halir (Sakkwato)
2. Bashir Yahuza Malumfashi (Katsina)
3. Bello Shehu Alkanci (Zamfara)
GASAR JA-IN-JA
1. Bello Muhammad Geɗawa (Sakkwato)
Tun da farko dai jami’ar ta saka gasar ce a Janairun bara, inda aka gayyaci marubuta wakokin hikima su rubuta waka wadda ta danganci al’amuran tsaro a Arewa.
Jami’in Kwamitin gasar, Farfesa Salisu Ahmad Yakasai ya shaida wa wakilinmu cewa mawaka sama da 100 suka shiga gasar daga sassa daban-daban na Najeriya.
Ya ce cikin mawakan sama da 100, an tace mutum 30, wadanda suka fafata a zagaye na karshe, inda aka yi bikin karrama zakaru daga na daya zuwa na uku.
Haka kuma, an gudanar da gasar tsarin wakar Ga-ni-ga-ka, inda aka ba mawaka maudu’in su rubuta waka mai baitoci 10 a kan Zaman Lafiya cikin minti 20.
A nan take aka kammala kuma ’yan takara sama da 40 suka fafata. Su ma aka sanar da zakaru uku da suka yi zarra.
A yayin rufewar, an gabatar da gasar Ja-in-ja, inda mawaka za su kalubalanci juna da baitoci kai tsaye a gaban jama’a.
Taron dai ya gudana ne a babban zauren taro na Jami’ar Usman Danfodiyo Sakkwato.