✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bar mata a baya a bangaren likita – Dokta Fatima Bello

Dokta Fatima Bello kwararriyar Likitar yara ce da take aiki a Asibitin kwararru na Jami’ar Usman danfodiyo da ke Sakkwato.  Aminiya ta zanta da ita…

Dokta Fatima Bello kwararriyar Likitar yara ce da take aiki a Asibitin kwararru na Jami’ar Usman danfodiyo da ke Sakkwato.  Aminiya ta zanta da ita a kan tarihinta da gwagwarmayar da ta sha kafin ta kawo wannan matsayi da yadda aka yi ta zama kwararriyar likita da sauran batutuwa da dama kamar haka:

Zamu so mu san takaitaccen tarihin rayuwar ki?
Ni ’yar asalin Jihar Kogi ce.  An haife ni a garin Sakkwato kuma na tashi a Sakkwato.  Na yi karamar makaranta a garin Sakkwato sannan na je babbar  makarantar ’yan mata da ke garin Illela, bayan shekara uku na koma Kwalejin ’yan mata ta kimiyya tsantsa da ke Sakkwato wato GGC inda na kammala kuma na  samu sakammako mai kyau wanda ya kai ni samun gurbin yin karatu a Jami’ar Sakkwato watau Usman danfodiyo, inda na yi karatu a fanin likitanci, kuma na fito kwararrar likita a fannim yara watau (pediatrics).   Bayan haka na yi housemanship na  shekara daya da kuma bautar kasa shi ma shekara daya duk a Sakkwato. Bayan da na fara aiki, na yi kwasa- kwasai da dama.   Na yi jarrabawar Junior da Senior Residency kuma na samu nasara har na kawo matsayin (consultant) Likitar da ake tuntuba a bangaren da ya shafi kula da lafiyar yara watau padiatrics.   Ina da aure da yara hudu.

 Mene ne dalilin ki na zaben wannan aikin?
Ainihi dai tun farko dai ba shi na so in yi ba, na so ne na zama lauya tun ina babbar makaranta.   Idan muna wasa ana tambayarmu me muke son mu  zama a rayuwa?  Na kan ce ina son na zuma lauya.    Ban ma san abin da ake karantawa a zama likita ba a wancan lokaci.  Bayan na kammala karatun sakandare, idan ana tambaya ta, sai na rika cewa ina son na karanci micro biology ko kuma biochemistry duk dai ba wai don na san abin da yake nufi ba. Iyayena suka fara maganar karatun likitanci, tun akan yayyena ake cewa ana son a karanta likitanci, amma da yake Allah Ya kaddara cewa hakan zai faru a kaina, iyaye na suka yi shawara da ni kan na  zabi wannan fannin.   Sai ga shi cikin ikon Allah na zama kwararrar likita a fannin lafiyar yara.

Ya kika ga yanayin ilimin mata?
A gaskiya idan za a yi la’akari daga inda muka fito za a ga cewa an dan samu cigaba sosai, saboda an yi ta kawo abubwa da dama don fahimtar da mata, wajen neman llimi, kuma an yi sa’a mutane da dama sun yi na’am da wannan tsarin, amma duk da haka akwai neman karin yawaituwar mata a fannoni daban daban na rayuwa, ba kuma komi ke kawo cikas wajen samun nasara a kan neman ilimin mata ba sai don irin al’adarmu ta rashin ganin muhimmancin ilimin mace.   A tunanin iyayenmu a da, da zarar mace ta girma to a gaggauta a yi mata aure.   Idan mace ba ta da ilimin da ya kamata ko a dakin auren ma za a iya tafka barna.  A takaice dai har yanzu ilimin mata bai taka kara ya karya ba, don haka akwai bukatar a kara bunkasa shi.

A fannin ki, ko akwai cigaba watau

mata dake wannan aikin?
A gaskiya akwai cigaba, amma ba sosai ba. Ba za mu kwatanta yadda mata suke yin gogayya da maza a fannin Likita ba, ma’ana maza sun yi mana zarra.  Wannan fannin ne ya kamata a ce akwai mata da yawa a ciki fiye da maza don, ga lada, kuma shi ne zavin da ya fi mana wajen rufin asirin kanmu da mata yan’uwanm don haka akwai buqatar iyaye su qara himma a kan ilimin  mata.

Ya kike yi wajen haxa aiki da rayuwar aure?
A bu ne mai sauqi.  Amma idan mace ta yanke shawarar rashin yiyuwar sa, to zai  zame mata mawuyacin al’amari.   A zuciyar ki idan kika qudurin yin aikin alhairi, kuma kika sa Allah gaba, to duk komai mai sauqi ne.   Ragwanci ne mace ta zauna babu sana’a, ba ilimi, ba aiki.   Ya zama wajibi, mu tashi  mu amfani al’umma da kuma gyara zamantakewar auren mu.   Mu ne gida, mu ne komai na iyalinmu, don haka kada mu yi sake wajen cimma burin mu na rayuwa.

Wadanne qalubale kike fuskanta ta dalin wannan aiki?
Kasancewata mace, shi kansa wani babban qalubale ne.  Kafin a gane ke wace ce sai kin sha wuya.   Kamar wurin aikin mu mataki-mataki ne.  Akwai karatun da ake yi watau  Junior da Senior Residency da kuma aiki a vangarori daban daban kafin mutum ya kai matsayin wanda za a riqa tuntuva (consultant).   Idan mace ta kai wannan matsayin za ta fuskantar qalubale daga vangaren maza, musamman idan kika kasance ke ce shugaba a fannin.  Dole sai kin daure kin jajirce don za ka ta cin karo da abubuwa da dama waxanda maza za su riqa yi miki da gangan don su hasala ki ko ku karya miki gwiwa, a wani lokacin ma don su nuna ba ki iya ko qwarewa ba.  Amma idan kika dage ba ki yi qasa a gwiwa ba, babu abin da zai razana ki,.  To wannan ma wani babban qalubale ne a aikin Likitan mata.

Wane cigaba kika samu?
Alhamdulillahi, da farko dai samu kwanciyar hankali da wadatar zuci, da kuma matsayin da Allah Ya ba ni wajen ceto rayuwar qananan yara cikin ikon Allah.

Ya kike son a riqa tunawa da ke?
Kan gaskiya da tsoron Allah.  Sannan ta hanyar kawo canji a rayuwar mutane.

Me kika fi so a rayuwa ?
 Yin karatu, saboda yanayin aiki na kullum ina cikin karatu ne, sai ya zamana na gina rayuwata kan haka.

Mene ne shawarar ki ga mata?
A ji tsoron Allah, don mu zama abin gwaji ga iyalan mu. Mu tabbatar da cewa mun kawo cigabain al’umma ba gurvacewarta ba. Mu bar tunanin cewa wani abin sai maza kawai, a a mu ma za mu iya yi da yardar Ubangiji.