Wasu fusatattun matasa a Masarautar Ofutop da ke Karamar Hukumar Ikom a Jihar Kuros Riba sun tattara sarakunansu tare da banka musu wuta.
Rahotanni sun ce da kyar da jibin goshi sarakunan suka tsira da rayuwarsu.
- Yadda aka ceto mata 4 masu ciki a gidan sayar da jarirai
- An cafke Uwar da ta sayar da jaririyarta ‘yar watanni 4 a Katsina
Wata majiya daga yankin ta shaida wa Aminiya cewa matasan sun yaudari sarakunan ne ta hanyar gayyatar su zuwa dandalin da mutanen kauyukan kan yi taro a kowace shekara domin tattauna matsalolin da suka shafe su.
Aminiya ta gano cewa rashin sani ya sanya sarakunan suka katse baccinsu suka baro dakunan iyalansu da misalin karfe 11.00 na dare.
Ashe tuni matasan sun tanadi man fetur wanda suka bulbula masu kuma nan take suka kyasta ashana suka jefa musu wuta ta kama.
Majiyar ta ci gaba da shaida wa Aminiya cewa matasan sun kona basaraken Emuru-Shima mai suna Ntun Ayan Ekum wanda ya sha da kyar.
Matasan dai na zargin sarakunan ne da yin sakaci wajen daukar mataki a kan yawan mace-macen da galibin matasan yankin ke yi na babu gaira babu dalili.
Mutuwar wani matashi mai suna Osim Ebuk Obim a yankin na daga cikin abun da ya tunzura lamarin, inda rahotanni suka nuna cewa matasan kauyen Isiele su ma sun yi yunkurin kona nasu sarkin.
Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kuros Riba, DSP Irene Ugbo ta shaida wa Aminiya cewa suna ci gaba da bincike, duk da cewa ba su kai ga kama kowa ba ya zuwa yanzu.
Sai dai ta ce da zarar sun samu nasarar cafke wadanda ake zargin ba za su yi wata-wata ba wajen hukunta su.