Al’ummar garin Deba hedkwatar Karamar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, sun yi tururuwa don halartar kasaitaccen hawan dabar da aka shirya wa Sarkin Deba Alhaji Ahmed Usman kan ba shi sanda mai daraja ta daya a zamansa na Sarkin Deba na II.
Gwama Ibrahim Dankwambo ne ya nada Alhaji Ahmed Usman Sarkin Deba a ranar 8 ga Agustan bara bayan rasuwar Sarkin Deba na farko Alhaji Abubakar Waziri Mahdi.
An daga darajar Masarautar Deba ne zuwa masarauta lokacin tsohuwar gwamnatin marigayi Alhaji Abubakar Habu Hashidu a shekarar 2000.
Dubban jama’ar garin ne da bakin da aka gayyato da suka hada da manyan kusoshin gwamnati da sarakuna daga ciki da wajen Jihar Gombe ne suka halarci garin Deba don halartat wannan kasaitaccen biki.
Da yake jawabi Gwamna Ibrahim Dankwambo, ya yi kira ga Sarkin da sauran masu rike da sarautun gargajiya cewa su tabbatar da dorewar zaman lafiya a yankunansu da kuma sanar da hukuma duk wanda ba a yarda da take-takensa ba. Sai ya yi wa Sarkin addu’ar alheri da fata a gudanar da zaben da ke tafe lami lafiya a jihar.
A jawabin godiya Sarkin Deba Alhaji Ahmed Usman, ya bayyana daga darajar masarautar da cewa abin alfahari ne gare shi da al’ummar Masarautar Deba baki daya.
Ya ce al’ummar Masarautar Deba suna cike da farin ciki kan karimcin Gwamna Ibrahim Dankwambo, kuma zai tabbatar da adalci da gaskiya wajen gudanar da mulki a tsakanin al’ummarsa.
Shugaban taron, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Alhaji Mahmud Yayale Ahmed, kira ya yi ga Sarkin da sauran sarakuna su taimaka wajen ci gaban siyasar Arewacin kasar nan don ganin an farfado da martabar yankin.
Alhaji Yayale Ahmed, ya shawarci sabon Sarkin kan ya kamanta adalci a tsakanin al’ummarsa kuma ya ji tsoron Allah a dukan al’amuransa.
Bayan ba shi sandar masu rike da sarautun gargajiya a masarautar sun yi hawan daba don burge Gwamnan da bakin da aka gayyato.