An ba mazauna tsoffin gidaje wa’adin kwana bakwai su fice ko a gurfanar da su gaban kuliya, a Jihar Oyo.
Gwamnatin a jihar ta ba da wa’adin ne ga mazauna irin gidajen da ke birnin Ibadan, cewa su hanzarta tattara nasu-ya-nasu su fice saboda yiwuwar rushewarsu da ke iya janyo hasarar rayuka.
Shugaban Karamar Hukumar Ibadan ta Arewa maso yamma, AbdulRahman Olanrewaju Adepoju ne ya ce, “Idan suka ki bin wannan umarni za mu tasa keyarsu zuwa kotu domin hukumta su.”
Ya ce lura da yadda katangogin gidajen suka rube bayan dadewa da gina su da tubalin kasa, ya zama dole a bayar da irin wannan wa’adin domin guje wa fadawa cikin matsala.
- Matashin da ya sare hannun kanen mahiafinsa ya shiga hannu
- Yadda aka yi Jana’izar Sarkin Gobir ba tare da gawarsa ba
Tawagar Shugaban Karamar Hukumar ta kai ziyarar ne domin yekuwar yiwuwar bullar cutar kwalara, amma sai yayi kicibis da wadannan gidaje da ya nuna damuwa a kan yadda mutane ke ci gaba da zama a cikinsu.
Dangane da yiwuwar bullar annobar kwalara a yankin kuwa, cewa ya yi “ya zama wajibi mu hanzarta daukar matakin riga kafi musamman saboda cutar ta riga ta bulla a jihohin kimanin 30.”
Alhaji AbdulRahman Adepoju wanda yake tare da jami’an kiwon lafiya a lokacin ziyarar, ya umarce su da su shiga cikin gidaje domin rufe dukkan gidan da aka gano sun ki kwashe kazantar makewayinsu.
Ya ce za a rufe irin wadannan gidaje ne a nan take har sai sun kawar da irin wannan kazanta.
Haka kuma ya bayar da umarnin rufe dukkan rijiyar da aka gina a kusa da makewayi ko magudanan ruwa domin kauce wa kamuwa da cutar kwalara a yankin.