✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ba da belin ma’ajin makaranta da ake zargi da kawalcin dalibansa

Kotun Shari’ar Musulunci ta Daya da ke Tudun Wada, Zariya ta bayar da belin Ma’ajin Sakandaren Gwamnati da ke Rimin Doko, Unguwar Kaura, Zariya, mai…

Kotun Shari’ar Musulunci ta Daya da ke Tudun Wada, Zariya ta bayar da belin Ma’ajin Sakandaren Gwamnati da ke Rimin Doko, Unguwar Kaura, Zariya, mai suna Dahiru Aminu da  abokinsa Bello Ahmed da ake zargi da yin kawalcin dalibansa mata.

Da yake bayyana matsayin kotun Mai shari’a Malam Iliyasu Umar Muhammadu ya ce ana tuhumarsu ne bisa sashi na 170 da sashi na 222 na kundin dokokin Jihar Kaduna.

Ya ce bisa laifin da ake tuhumarsu, kotu ta bayar da belinsu da sharadin swani limamin Juma’a ko babban hakimi ne zai tsaya musu, kuma ta tsayar da ranar 29 ga Janairun nan don ci gaba da sauraron karar.

Dahiru Aminu a Unguwar Kusfa cikin Zariya ana zargin yana amfani da matsayinsa a makarantar ce inda yake daukar dalibai ’yan mata yana kai wa wani mai suna Bello Ahmed a wani daki da ke Unguwar Gyallesu a Tudun Wada, Zariya.

’Yan sanda sun gurfanar da mutanen biyu ne a gaban kotun a ranar Juma’ar makon jiya bayan sun amsa laifin da suke tuhumarsu da aikatawa, inda kotun ta tasa keyarsu zuwa gidan yari kafin a kawo su ranar Litinin da ta gabata don ci gaba da sauraran karar.

A lokacin da Aminiya ta ziyarci kotun don ganin yadda shari’ar za ta kaya a ranar Litinin dai da ta gabata ta yi kicibis da daya daga cikin mahaifan daliban a ofishin babban mai binciken laifuffuka na hadikwatar ’yan sanda shiyyar Tudun Wada, inda ya ce ba su son a ci gaba da shari’ar don haka sun zo su janye karar ce sakamakon sulhuntawa da bangarorin biyu suka yi a gida.