✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An aika wani sako da ake zargin bam ne zuwa ga Obama da Hillary

An aika wani abu da ake zargin bam ne ga tsohon Shugaban Amurka Barack Obama da tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton, kamar yadda…

An aika wani abu da ake zargin bam ne ga tsohon Shugaban Amurka Barack Obama da tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton, kamar yadda ta bayyana.

Wannan yana zuwa ne kwana biyu bayan an tsinci bam a gidan fitaccen dan kasuwa George Soros a wajen birnin New York.

Wadansu masana masu kula da sakonnin da ake aike wa tsofaffin jami’an Amurka ne suka gano haka.

Sai dai zuwa yanzu ba a san wurin da aka gano sakon ba tukunna.

Sakon farko dai an aika shi ga adireshin Misis Clinton ne a ranar 23 ga Oktoban nan, kamar yadda hukumomin tsaron sirrin Amurka suka bayyana.

“A safiyar yau, (shekaranjya) 24 ga Oktoba, aka aike da sako na biyu ga Barack Obama amma jami’an tsaron sirrin kasar sun bankado shi a birnin Washington DC,” inji wata sanarwa daga hukumar tsaron sirrin kasar.

“Duka sakonnin an bankado su ne kafin a aike wa wadanda aka nufa da su,” inji sanarwar.

Kwanakin baya Aminiya ta ruwaito yadda aka aike da sako makamancin haka zuwa ga Shugaban Amurka Donald Trump.