✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka za ta tura sojoji 300 zuwa Kamaru

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ce zai tura sojoji 300 zuwa kasar Kamaru domin taimaka mata wajen yaki da kungiyar Boko Haram.Wata sanarwa da…

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ce zai tura sojoji 300 zuwa kasar Kamaru domin taimaka mata wajen yaki da kungiyar Boko Haram.
Wata sanarwa da ta fito daga fadar Shugaban Amurka ta White House ta ce, Shugaba Obama ya bayyana niyyarsa ga Majalisar Dokokin kasar cewa zai tura dakaru 300, a yunkurin kawo karshen ayyukan ta’addanci na kungiyar Boko Haram.
Wani jami’in gwamantin Amurka da ya bukaci a boye sunansa, ya tabbatar wa gidan rediyon BBC cewa wasu kwamandojin rundunar sojin Amurka har sun isa Kamaru.
Ya kara da cewa, dakarun za su dukufa ga aikin tattaro bayanan sirri da cikakkun bincike a kan yadda ake gudanar da aikin kawo karshen hare-haren mayakan Boko Haram.
kungiyar Boko Haram dai ta addabi kasashen Najeriya da Kamaru da Chadi da Nijar da inda ta hallaka akalla fiye da mutum dubu 15, a cikin shekara shida da suka gabata.
kasashen gabar Tafkin Chadi wato Najeriya da Kamaru da Chadi da Nijar dama sun dade suna neman taimakon manyan kasashen duniya domin kawar da kungiyar Boko Haram.